Shugaba Pezeshkian ya ce duk wanda ya kai hari ga Jagoran Addini zai tayar da babban yaƙi. Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za ta mayar da martani mai tsanani ga duk wata ƙasa da ta kuskura ta kai hari kan Jagoran Addinin Iran, Ali Khamenei. Ya ce irin wannan hari zai zama tamkar ƙaddamar da babban yaƙi ne kan Iran. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya jaddada cewa Iran ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na kai hari ga babban jagoranta ba. Haka kuma, ya zargi Amurka da ƙawayenta da haddasa matsin tattalin arzikin da Iran ke ciki, yana mai cewa takunkuman da aka daɗe ana kakabawa ƙasar sun jefa al’ummar Iran cikin mawuyacin hali. Gargaɗin nasa ya zo ne bayan tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Khamenei a matsayin “mutum mara lafiya” a wata hira da ya yi, inda ya kuma soki yanayin rayuwa a Iran tare da cewa ƙasar na buƙatar sabbin shugabanni. Tushen labari: Newstimehub
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Iran Ta Yi Gargadi Kan Duk Wani Hari Ga Khamenei
Shugaba Pezeshkian ya ce duk wanda ya kai hari ga Jagoran Addini zai tayar da babban yaƙi. Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za ta mayar da martani mai tsanani ga duk wata ƙasa da ta kuskura ta kai hari kan Jagoran Addinin Iran, Ali Khamenei. Ya ce irin wannan hari zai...

At a glance