Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Sabbin hare-hare sun girgiza Beirut da Tehran yayin rikicin Gabas ta Tsakiya

Iran ta kai hari Dubai, farashin mai ya haura dala 100 kan kowace ganga Ƙarar fashewar abubuwa ta karaɗe birnin Beirut na Lebanon da sanyin safiyar Litinin bayan Isra’ila ta kai sabbin hare-hare kan birnin, yayin da ita ma ta kai hare-hare a Tehran babban birnin Iran. Rikicin ya kara tsananta tun...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:12
Sabbin hare-hare sun girgiza Beirut da Tehran yayin rikicin Gabas ta Tsakiya
De un vistazo

Iran ta kai hari Dubai, farashin mai ya haura dala 100 kan kowace ganga Ƙarar fashewar abubuwa ta karaɗe birnin Beirut na Lebanon da sanyin safiyar Litinin bayan Isra’ila ta kai sabbin hare-hare kan birnin, yayin da ita ma ta kai hare-hare a Tehran babban birnin Iran. Rikicin ya kara tsananta tun...

Iran ta kai hari Dubai, farashin mai ya haura dala 100 kan kowace ganga Ƙarar fashewar abubuwa ta karaɗe birnin Beirut na Lebanon da sanyin safiyar Litinin bayan Isra’ila ta kai sabbin hare-hare kan birnin, yayin da ita ma ta kai hare-hare a Tehran babban birnin Iran. Rikicin ya kara tsananta tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare kan Iran kusan makonni biyu da suka gabata. Tun daga lokacin, Iran ta mayar da martani da kai hare-hare kan Isra’ila da sansanonin Amurka da kuma wasu kayayyakin makamashi na ƙasashen Larabawa da ke gaɓar teku ta amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa. Ta kuma katse jigilar kayayyaki ta mashigin ruwan Hormuz, lamarin da ya haddasa fargaba kan yiwuwar rikicin makamashi a duniya. Farashin ɗanyen mai na Brent ya haura dala 100 kan kowace ganga a kasuwar duniya, inda ya kai kusan dala 104 a farkon cinikayya ranar Litinin, bayan ya ƙaru sosai tun bayan fara rikicin. A wani lamari daban, wani jirgi mara matuƙi ya afka wa tankar mai kusa da filin jiragen sama na Dubai, wanda ya haddasa gobara tare da tilasta rufe filin jirgin na ɗan lokaci, duk da cewa ba a samu rahoton asarar rai ba. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya bukaci wasu ƙasashe su tura jiragen ruwan yaƙi domin tabbatar da buɗe mashigin Hormuz, amma har yanzu ba a samu tabbacin amincewar ƙasashen da ya ambata ba. A Lebanon kuwa, hare-haren Isra’ila sun tilasta dubban mutane barin gidajensu, yayin da rahotanni suka nuna cewa daruruwan mutane sun mutu a rikicin da ke kara tsananta a yankin. Tushen labari: Newstimehub