Na'urorin mahukuntan Tel Aviv sun kakkaɓo jirage maras matuƙa da makamai masu linzami da Iran ta harba Isra'ila a yayin da Tehran ya ce zai kai hari na gana a Jordan, sannan ya gargaɗi Amurka da ta guji shiga sharo-ba-shanu. Iran ta ƙaddamar da hare-hare a Isra'ila ranar Asabar da tsakar dare, inda ta harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 200. Iran ta kai waɗannan hare-haren ramuwar gayya ne bayan Isra'ila ta kai hari a ofishin jakadancinta da ke Syria, inda ta kashe zaratan sojinta bakwai ciki har da masu muƙamin janar. Jirage marasa matuƙa da makamai masu linzamin da Iran ta harba shi ne karon farko da take kai hari Isra'ila kai-tsaye daga cikin ƙasarta. Waɗannan hare-hare sun jawo fargaba game da yiwuwar ramuwa daga Isra'ila kan Iran lamarin da zai ƙara zaman ɗar-ɗar ɗin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya a Isra'ila
Na'urorin mahukuntan Tel Aviv sun kakkaɓo jirage maras matuƙa da makamai masu linzami da Iran ta harba Isra'ila a yayin da Tehran ya ce zai kai hari na gana a Jordan, sannan ya gargaɗi Amurka da ta guji shiga sharo-ba-shanu. Iran ta ƙaddamar da hare-hare a Isra'ila ranar Asabar da tsakar dare, in...

At a glance