Shawarar na zuwa yayin tashin hankali a yankin ya ƙaru Rahotanni sun nuna cewa Iran na tunanin saka kuɗin da jiragen ruwa za su riƙa biya domin wucewa ta Mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar makamashi a duniya. An ce an gabatar da daftarin doka da zai tilasta jiragen ruwa da ƙasashen da ke amfani da mashigin su biya kuɗi da haraji ga Iran domin samun tsaro yayin wucewa. Wani ɗan majalisar Iran ya bayyana cewa ƙasashen da ke cin moriyar tsaron mashigin ya kamata su biya kuɗi saboda muhimmancin hanyar ga kasuwancin duniya. Shawarar na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila ke ƙaruwa, lamarin da ya kusa janyo rufe mashigin gaba ɗaya. Mashigin Hormuz na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai a duniya, inda kusan kashi 20 cikin 100 na man duniya da iskar gas ke wucewa ta cikinsa kullum. Matakin na iya ƙara tashin hankali a kasuwannin makamashi da kuma tasiri ga tattalin arzikin duniya. Tushen labari: Newstimehub
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Iran na duba yi wa jiragen ruwa kuɗin wucewa Hormuz
Shawarar na zuwa yayin tashin hankali a yankin ya ƙaru Rahotanni sun nuna cewa Iran na tunanin saka kuɗin da jiragen ruwa za su riƙa biya domin wucewa ta Mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar makamashi a duniya. An ce an gabatar da daftarin doka da zai tilasta jiragen ruwa da ƙasashen d...

Em resumo