Hukumar ta ce za a buɗe rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta ta hanyar tasharta, cvr.inecnigeria.org. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya ta ce za a fara gudanar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a na shekarar 2025 a duk faɗin ƙasar a ranar 18 ga watan Agusta. INEC ta bayyana hakan ne a shafinta na X ranar Juma'a. Hukumar ta ce za a buɗe rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta ta hanyar tasharta, cvr.inecnigeria.org. Ya bayyana cewa za a fara rajistar mutanen nan da mako guda, ranar 25 ga watan Agusta. A cewarta, za a gudanar da wannan aiki a duk fadin kasar a dukkan ofisoshin kananan hukumomin da kuma wuraren da aka keɓe. INEC ta ce za a gudanar da aikin ne daga ranar Litinin zuwa Juma'a, daga karfe 9 na safe zuwa karfe 3 na rana. "Kuri'unku sun ta’allaƙa ne da yin rajistarku. Ka da ku rasa damarku ta yin rajista," in ji shi. A bisa ƙa’ida ‘yan shekara 18 zuwa sama ne kawai ke da izinin yin zaɓe a Nijeriya. A shekarar 2027 ne za a sake yin manyan zaɓuka a Nijeriya.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
INEC za ta fara rajistar masu zaɓe a faɗin Nijeriya ranar 18 ga Agustan 2025
Hukumar ta ce za a buɗe rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta ta hanyar tasharta, cvr.inecnigeria.org. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya ta ce za a fara gudanar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a na shekarar 2025 a duk faɗin ƙasar a ranar 18 ga watan Agusta. INEC ta bay...
At a glance