Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Hisbah ta ce za ta gurfanar da Murja Kunya a gaban kotu

Shugaban Hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa za a gurfanar da ita ne kan tuhume-tuhumen yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta. Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce za ta gurfanar da fitacciyar ’yar TikTok Murja Ibrahim Kunya a gaban kotu. Shugaban Hukumar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:12
Hisbah ta ce za ta gurfanar da Murja Kunya a gaban kotu
At a glance

Shugaban Hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa za a gurfanar da ita ne kan tuhume-tuhumen yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta. Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce za ta gurfanar da fitacciyar ’yar TikTok Murja Ibrahim Kunya a gaban kotu. Shugaban Hukumar...

Shugaban Hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa za a gurfanar da ita ne kan tuhume-tuhumen yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta. Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce za ta gurfanar da fitacciyar ’yar TikTok Murja Ibrahim Kunya a gaban kotu. Shugaban Hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa za a gurfanar da ita ne kan tuhume-tuhumen yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta. Murja ta shahara musamman a shafukan sada zumunta inda take da miliyoyin mabiya, inda ake ganin tana yawan jawo ce-ce-ku-ce. A shekarar 2023 ne wata kotu a Kano ta taɓa tura Murja da wasu yan TikTok zuwa gidan gyaran hali. Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta Hisbah gayyaci Murja domin ja mata kunne. Haka ma a kwanakin baya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce zai saka ta cikin jerin waɗanda za a yi wa auren zawarawa a Kano.