Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Hira: 'Na yi ta komawa Gaza saboda za mu iya kawo sauyi'

Steve Sosebee, wanda aka karrama da lambar yabo ta TRT ta Rayuwa, ya yi magana game da jajircewarsa na ba da agaji ga yaran Falasdinu duk da asarar rai da barna. A watan Janairu, Steve Sosebee, wanda aka lullube shi da keffiyeh, ya karɓi lambar yabo ta TRT ta Nasarar Rayuwa na shekaru da yawa na...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:12
Hira: 'Na yi ta komawa Gaza saboda za mu iya kawo sauyi'
Кратко

Steve Sosebee, wanda aka karrama da lambar yabo ta TRT ta Rayuwa, ya yi magana game da jajircewarsa na ba da agaji ga yaran Falasdinu duk da asarar rai da barna. A watan Janairu, Steve Sosebee, wanda aka lullube shi da keffiyeh, ya karɓi lambar yabo ta TRT ta Nasarar Rayuwa na shekaru da yawa na...

Steve Sosebee, wanda aka karrama da lambar yabo ta TRT ta Rayuwa, ya yi magana game da jajircewarsa na ba da agaji ga yaran Falasdinu duk da asarar rai da barna. A watan Janairu, Steve Sosebee, wanda aka lullube shi da keffiyeh, ya karɓi lambar yabo ta TRT ta Nasarar Rayuwa na shekaru da yawa na ayyukan jinƙai a Falasdinu. "Ba ku kadai ba ne cikin wannan halin," in ji shi, yana nufin Falasdinawa yayin da ya karbi lambar yabo don nuna godiya ga aikinsa. Sosebee ya yi watsi da kudin goro da ake yi wa wasu al'amura ta hanyar jajircewarsa, musamman ga yaran Falasdinawa a fuskar zaluncin Isra'ila na tsawon shekaru da dama. A shekarar 1991, tare da marigayiyar matarsa, Huda Al Masri, ya kafa Asusun Tallafa wa Yara na Falasdinu (PCRF) don ba da kulawar jinya, agajin jinƙai, da tallafi ga Falasdinawa. A ci gaba da aikinsa, a cikin 2024, Sosebee ya kafa HEAL Palestine, wanda ke mayar da hankali kan Lafiya, Ilimi, Taimako, da Jagoranci don taimaka wa yara da iyalai masu bukata. Ta kokarinsa na rashin gajiyawa, ya taimaka wa yara Falasdinawa sama da 2,000 don su sami kulawar ceton rai a kan iyakokin kasa da kasa. "Kisan kiyashi na farkar da mutane su gane me ke faruwa," in ji shi a cikin wata tattaunawa ta musamman da TRT World, yayin da yake waiwaye kan ayyukansa, wato shirin HEAL Palestine, da kuma buƙatar gaggawa ta duniya. An gina shi shirin HEAL Palestine a kan ginshiƙai huɗu masu muhimmanci: lafiya, ilimi, taimako, da jagoranci. Kungiyar tana ba da tallafin kula da lafiyar kwakwalwa kuma tana gudanar da wani asibiti a Gaza, tana ba da tallafin karatu ga ɗalibai, kuma tana gudanar da wuraren dafa abinci waɗanda ke ciyar da dubban mutane. Har ila yau, tana taka muhimmiyar rawa wajen isar da kayayyakin jinya da taimakon jin kai, musamman a arewacin Gaza. TRT World ta zanta da Steve kuma ga yadda abin ya kasance. TRT World: Ta yaya kuka fito da manufar kafa kungiyar ba da agaji ga yaran Falasdinu? Steve Sosebee: Na fara ziyartar Falasdinu ne a shekarar 1988. A lokacin Intifada na farko ne. A matsayinmu na ɗaliban aikin jarida, mun zagaya a Yammacin Kogin Jordan da Gaza, kuma mun sadu da iyalai kuma muka ga yadda rayuwarsu ta kasance. Na kamu da son al'adu da mutanen yankin lokacin da na ga gagarumar gwagwarmayarsu. Wannan tafiya ta sauya rayuwata. Da farko, na yi aiki a matsayin ɗan jarida don ilimantar da Amurkawa game da ainihin abubuwan da ke faruwa a can—hakikanin da ba a san su ba a Amurka a lokacin. Ba na jin yawancin Amurkawa sun san tsananin mamaya da kisan ƙabilanci da ake yi. A gare ni, rayuwa ta ɗauki hanya dabam don isa ga al'umma ɗaya. Komai ya sauya sa’ad da na shirya kula da wani ɗan’uwa da ’yar’uwa da suka ji rauni a wani harin bam a Yammacin Kogin Jordan. Na kawo su Ohio don jinya, kuma ya yi tasiri sosai - ba kawai a gare su ba, amma ga dukan al'umma. Al'ummar Falastinu, al'ummar Larabawa, sun yi ƙoƙarin daukar matakan cigaba wajen kula da su. Lokaci ne na haɗin kan ɗan'adam. Mutane sun nuna tausayi kuma sun taru don sanin halin da yara ke ciki. Shi ke nan lokacin da na gane aikin jinƙai na iya zama abu mai ƙarfi don sauyin. Wadannan yara, da a baya ba a fahimci suna cikin wadanda bala'in ke shafa ba, a yanzu halin da suke ciki ya bayyana ga mutane. Labaran nasu sun dauki hankula. Kuma a karon farko, Amurkawa da yawa suna ganin yaran Falasdinawa a matsayin mutane - masu murmushi, dariya, masu rai, yara masu numfashi - kuma ba nau'in wulakantattun da a da suke gani ba a matsayin wadanda zai iya yin hadin gwiwa wajen aiwatar da kisan kare dangi. TRT Hausa: Yaya kuke kallon yadda kafafen yada labaran Yamma ke kallon Falasdinawa? Sosebee: Sosebee: D gangan ake wulakanta Falasdinawa. Hanya guda daya tilo da za a iya aiwatar da kazamin zalunci ga yaran Gaza, ita ce idan mutane suka dauke su a matsayin ba 'yan'adam. Kuma kafafen yada labarai sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da wannan fahimta. Ko a yau, labaran da ake watsa na son rai ne. An ba da rahotanni iri ɗaya daban-daban ya danganta da wanda abin ya shafa, wato Isra'ilawa ko Falasɗinawa. Kafofin watsa labarai na yau da kullum ko The New York Times ko CNN suna ci gaba da tace gaskiya tare da ƙara bincike na zahiri ga wata manufa: kashe yara ba daidai ba ne. Amma duk da haka akwai hujjar hakan a cikin manyan kafofin watsa labarai na Amurka. Ko da yake yanayin kafofin watsa labarai sun sauya. Kuma tasoshi kamar TRT World, 'yan jarida masu zaman kansu, da masu ba da rahoto na ƙasa sun ƙyale mutane su ga ainihin gaskiya - wani abu da sauran kafafen watsa labarai ba sa tacewa ko kuma karkatarwa. Don haka ne ake kai wa ‘yan jaridar Falasdinawa hari don nuna gaskiya. Suna cikin ainihin jaruman wannan rikicin, tare da likitoci, ma'aikatan jinya, da masu ba da amsa na farko.