Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Hauhawar farashi ta ragu zuwa kashi 23.5 cikin 100 a Ghana

Hukumar ƙididdiga ta Ghana ce ta tabbatar da raguwar inda ta ce an samu raguwar ne a watan Janairu 2025 idan aka kwatanta da watan Disamban 2024. Hauhawar farashi a Ghana ta ragu zuwa kashi 23.5 cikin 100 daga kashi 23.8 idan aka kwatanta da watan Disamban 2024, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta G...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:12
Hauhawar farashi ta ragu zuwa kashi 23.5 cikin 100 a Ghana
En bref

Hukumar ƙididdiga ta Ghana ce ta tabbatar da raguwar inda ta ce an samu raguwar ne a watan Janairu 2025 idan aka kwatanta da watan Disamban 2024. Hauhawar farashi a Ghana ta ragu zuwa kashi 23.5 cikin 100 daga kashi 23.8 idan aka kwatanta da watan Disamban 2024, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta G...

Hukumar ƙididdiga ta Ghana ce ta tabbatar da raguwar inda ta ce an samu raguwar ne a watan Janairu 2025 idan aka kwatanta da watan Disamban 2024. Hauhawar farashi a Ghana ta ragu zuwa kashi 23.5 cikin 100 daga kashi 23.8 idan aka kwatanta da watan Disamban 2024, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta Ghana GSS ta tabbatar a ranar Litinin. Farashin kayayyakin abinci a watan Janairun na kan 252.6 idan aka kwatanta da 204.5 a Janairun 2024. Haka kuma hukumar ta GSS ta bayyana cewa hauhawar farashi na wata-wata tsakanin Disamban 2024 zuwa Janairun 2025 na kan kashi 1.7 cikin 100. Hauhawar farashin kayayyakin abinci ya kasance abu mai muhimmanci inda ya kai 28.3 a watan Janairu, wanda hakan ke nufin an samu ƙaruwa da 2.06. Haka kuma hauhawar farashin da ba ta kayan abinci ba ta kasance a kan kashi 20.3 wanda hakan ya nuna an samu madaidaiciyar ƙaruwa da kaso 1.4 idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Hauhawar farashi a kan kayayyakin da aka samar a cikin ƙasa na kan kashi 25.7 a Janairu, inda kuma hauhawar farashi ga kayayyakin da aka shigar da su ƙasar ya tsaya a kan kashi 18.4. Kasar da ke yammacin Afirka na farfaɗowa ne daga matsalar tattalin arziki mafi muni a tsawon lokaci, tare da tashe-tashen hankula a masana'antun koko da na zinare. Duk da haka, hauhawar farashin ƙasar ya kasance fiye da kashi 8 na Bankin Ghana tare da tazarar maki 2 cikin 100 na kowane bangare. Babban bankin ya ce a makon da ya gabata zai dauki lokaci mai tsawo kafin hauhawar farashin kaya ya dawo tsakanin kashi 6 zuwa 10 cikin 100.