Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Hauhawar farashi a Nijeriya ta ƙaru zuwa kashi 31.7% a Fabrairu

Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar. A Nijeriya, hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru zuwa kashi 31.7% a watan Fabrairu, saɓanin kashi 29.90% da aka gani a Janairu, a cewar bayanan da suka fito ranar Juma'a daga cibiyar ƙididdiga ta ƙasar, Nigeria’s Bureau of Statistics (N...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:12
Hauhawar farashi a Nijeriya ta ƙaru zuwa kashi 31.7% a Fabrairu
En bref

Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar. A Nijeriya, hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru zuwa kashi 31.7% a watan Fabrairu, saɓanin kashi 29.90% da aka gani a Janairu, a cewar bayanan da suka fito ranar Juma'a daga cibiyar ƙididdiga ta ƙasar, Nigeria’s Bureau of Statistics (N...

Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar. A Nijeriya, hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru zuwa kashi 31.7% a watan Fabrairu, saɓanin kashi 29.90% da aka gani a Janairu, a cewar bayanan da suka fito ranar Juma'a daga cibiyar ƙididdiga ta ƙasar, Nigeria’s Bureau of Statistics (NBS). Sanarwar ta ce, "Duba da sauyin, hauhawar farashi a Fabrairun 2024 ya nuna ƙaruwar maki kashi 1.80%, idan an kwatanta da Janairun 2024". Bayanan sun nuna cewa a ma'aunin shekara bi-da-bi, hauhawar farashi a Nijeriya ya kasance da ƙarin kashi 9.79%, idan an kwatanta da kashi 21.91% da aka samu a Fabrairun 2023. NBS ta ce, “Wannan na nuna cewa hauhawar farashin a matakin shekara bi-da-bi ya ƙaru a Fabrairun 2024, idan aka kwatanta da irin wannan watan a shekarar da ta gabata (wato, Fabrairun 2023)”. Haka nan kuma, hauhawar farashin kayan abinci a Fabrairu ya kasance 37.92% a matakin shekara bi-da-bi. Wannan ya kasance da ƙarin kashi 13.57% idan an kwatanta da yadda aka gani a Fabrairun 2023 (24.35%), a cewar rahoton. Tun a baya, ƙaruwar tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar. Sai dai kuma, gwamnatin Nijeriya ta tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa za ta magance waɗannan matsaloli .