Ma’aikatan jinya huɗu na cikin waɗanda suka mutu a harin RSF a Sudan Aƙalla mutane 22, ciki har da ma’aikatan jinya huɗu, sun mutu yayin da wasu takwas suka jikkata bayan rundunar RSF ta kai harin bam a asibitin soji na Al-Kuweik a jihar Kudancin Kordofan ta Sudan, a cewar wata ƙungiyar likitoci. TRT Hausa Ƙungiyar likitocin Sudan ta ce harin ya kashe daraktan asibitin da wasu ma’aikatan jinya uku, tare da bayyana kai hari kan cibiyar jinya a matsayin laifin yaƙi da kuma keta dokokin ƙasa da ƙasa da ke kare fararen-hula da wuraren jinya. TRT Hausa Ta ƙara da cewa jerin hare-haren da ake kaiwa a jihar Kudancin Kordofan sun tilasta dakatar da ayyuka a wasu asibitoci, lamarin da ya ƙara tsananta matsalar jinƙai da barazana ga samar da kulawar lafiya ga fararen-hula. TRT Hausa Ƙungiyar ta ɗora alhakin harin kan RSF, tare da kira ga ƙasashen duniya, Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama su ɗauki mataki gaggawa, yayin da rikicin Sudan ke ci gaba da hallaka dubban mutane tun ɓarkewarsa a Afrilun 2023. TRT Hausa
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Harin bam ya kashe 22 a asibitin soji a Kudancin Kordofan
Ma’aikatan jinya huɗu na cikin waɗanda suka mutu a harin RSF a Sudan Aƙalla mutane 22, ciki har da ma’aikatan jinya huɗu, sun mutu yayin da wasu takwas suka jikkata bayan rundunar RSF ta kai harin bam a asibitin soji na Al-Kuweik a jihar Kudancin Kordofan ta Sudan, a cewar wata ƙungiyar likitoci....

A taƙaice