Hukumomi sun faɗa ranar Alhamis cewa aƙalla mutum 19 ne suka halaka a wani harin bam da ya faru a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya. Wani bam da ya fashe a wajen mai shayi da ke wani ƙauye a jihar Bornon Nijeriya ya kashe mutane, kuma ya raunata mutane sama da 20. Wannan shi ne hari na biyu cikin 'yan makonnin nan, a cewar majiyoyin tsaro ranar Alhamis. Fashewar ta auku ne a ƙauyen Kawuri na jihar Borno a yammacin Laraba, kuma ya kasanace cikin mafi munin hari a 'yan shekarun nana a arewa maso gabasin Nijeriya, yankin da a rikcin ta'addanci ya ragu ba kamar a shekarun baya ba. "An samu wata fashewa a wajen mai shayi a Kawuri da kimanin ƙarfe 8 na daren jiya. Mun kwashe gawarwaki 19 da masu raunuka 27," cewar Ibrahim Liman, wani ɗan sintiri da ke aiki da sojoji don yaƙi da ƙungiyoyin ta'adda ya faɗa wa AFP. Wasu 'yan sintirin sun tabbatar da adadin mutanen da harin Kawuri ya shafa. Kauyen yana da nisan kilomita 50 daga babban birnin jihar, Maiduguri. Ɗan ƙunar baƙin-wake Wani kwamandan 'yan sintirin da ke Kawuri, Kurmi Challume, ya ce ɗan ƙunan baƙin wake ne ya kai harin, inda ya kashe mutane 10. Babu ƙungiyar da ta ɗaukin alhakin harin na Laraba, amma ƙungiyar Boko Haram da takwarorinsu na ISWAP, suna ayyuka a jihar ta Borno. Gwamnan jihar Borno ya kafa dokar hana zirga-zirga ta awa 24 ranar Alhamis, bayan harin, cewar wata sanarwar 'yan sanda. An sanya dokar ne yayin da 'yan Nijeriya ke zanga-zanga a faɗin ƙasar don kokawa kan tsadar rayuwa, ciki har da a garin Maiduguri da babban birnin ƙasar Abuja. 'Harin ba-zata' Har yanzu 'yan ta'adda suna kai hare-hare da yin kwanton-ɓauna, da saka bam a gefen tituna, da garkuwa da mutane daga maɓoyarsu da ke yankunan karkara, amma harin bam a birane da ƙauyuka ya ragu a yankin na arewa maso gabas. "Boko Haram ta kai hari a Kawuri a daren jiya. Sun shammace mu saboda an daɗe ba a samu irin wannan hari ba," cewar Babakura Kolo, wani kwamandan ƙungiyar sintiri ya faɗa wa AFP. Ya ce an kai waɗanda suna samu raunuka zuwa asibitoci a birnin Maiduguri. Hukumomin soji ba su amsa neman tabbatar da labarin da aka tura musu ba. Harin na Kawuri ya zo ne makonnin bayan wasu 'yan ƙunar baƙin wake sun kashe mutane 32 a garin Gwoza na jihar ta Borno, lokacin da suka kai hari a wajen ɗaurin aure, da asibiti, da kuma wajen jana'iza.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Harin bam ya kashe mutum 19 a jihar Borno ta Nijeriya
Hukumomi sun faɗa ranar Alhamis cewa aƙalla mutum 19 ne suka halaka a wani harin bam da ya faru a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya. Wani bam da ya fashe a wajen mai shayi da ke wani ƙauye a jihar Bornon Nijeriya ya kashe mutane, kuma ya raunata mutane sama da 20. Wannan shi ne hari...

At a glance
Hukumomi sun faɗa ranar Alhamis cewa aƙalla mutum 19 ne suka halaka a wani harin bam da ya faru a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya. Wani bam da ya fashe a wajen mai shayi da ke wani ƙauye a jihar Bornon Nijeriya ya kashe mutane, kuma ya raunata mutane sama da 20. Wannan shi ne hari...
