“Wajibi ne a hukunta wadanda suka aikata irin wadannan laifuffuka a karkashin dokokin kasa da kasa,” in ji shugaban kasar Turkiyya Erdogan a jawabinsa a taron sauyin yanayi na MDD na shekarar 2023 a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza a matsayin "laifi na yaƙi da cin zarafin bil'adama." "Abin da ke faruwa a Gaza laifi ne na yaƙi, laifin cin zarafin bil'adama ne. Dole ne a hukunta wadanda suka aikata irin wadannan laifuka a karkashin dokokin kasa da kasa," in ji Shugaba Erdogan a jawabin da ya gabatar a wajen taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya na shekara ta 2023 a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, (UAE) a ranar Juma'a. A hare-haren da Isra'ila ta kai ta kashe Falasdinawa sama da 16,000, yawancinsu mata da kananan yara, kuma ba ta da wata hujja ta kare kanta a aikata hakan, in ji Erdogan. Ya kara da cewa, Turkiyya na tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya a duk cikin rikice-rikicen da ake fama da su, kuma tana kokarin samar da mafita mai adalci.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza laifi ne na cin zalin bil'adama: Shugaba Erdogan
“Wajibi ne a hukunta wadanda suka aikata irin wadannan laifuffuka a karkashin dokokin kasa da kasa,” in ji shugaban kasar Turkiyya Erdogan a jawabinsa a taron sauyin yanayi na MDD na shekarar 2023 a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyan...

A taƙaice