Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Har yanzu ba mu samu labarin fitar Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinmu ba - ECOWAS

Kungiyar ECOWAS ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba. Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:12
Har yanzu ba mu samu labarin fitar Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinmu ba - ECOWAS
A taƙaice

Kungiyar ECOWAS ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba. Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na...

Kungiyar ECOWAS ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba. Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba. A ranar Lahadi da hantsi kasashen uku suka fitar da sanarwa cewa sun fice daga kungiyar saboda ta gaza taimaka musu wurin shawo kan rashin tsaron da ke addabasu da ma sauran kalubalen da suke fama da su. "Har yanzu Hukumar ECOWAS ba ta samu bayani a hukumance daga kasashen uku ba da ke nuna cewa sun fita daga cikinta," a cewar wata sanarwa da ECOWAS ta wallafa a shafinta na X. Nijar, Burkina Faso da Mali sun fice daga ECOWAS Kungiyar ta ce ta yi mamakin "wannan mataki." ECOWAS Communique on Burkina Faso, Mali & Niger pic.twitter.com/5knRzXXKnz — Ecowas - Cedeao (@ecowas_cedeao) January 28, 2024 ECOWAS ta kara da cewa tana "aiki babu kakkautawa da wadannan kasashe domin ganin an dawo da tsarin mulki."