Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Hamas ta shirya sakin duk fursunonin da ke hannunta a lokaci guda ƙarƙashin yarjejeniyar Gaza

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 32 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,291, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025 1300 GMT — Wani babban jami'in Hamas ya shaida wa k...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:12
Hamas ta shirya sakin duk fursunonin da ke hannunta a lokaci guda ƙarƙashin yarjejeniyar Gaza
At a glance

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 32 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,291, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025 1300 GMT — Wani babban jami'in Hamas ya shaida wa k...

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 32 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,291, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025 1300 GMT — Wani babban jami'in Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu a shirye take ta sako dukkan sauran mutanen da suka yi garkuwa da su a lokaci ɗaya a mataki na biyu na tsagaita wuta a Gaza. Taher al-Nunu ya ce "Mun sanar da masu shiga tsakani cewa kungiyar Hamas a shirye take ta sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a tashi daya a kashi na biyu na yarjejeniyar, maimakon a dinga yin hakan a mataki-mataki, kamar yadda ake yi a matakin farko na yanzu." 2011 GMT — Isra'ila ta sace Falasɗinawa aƙalla 30 a samamen da ta kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa aƙalla 30 a samamen da suka kai wasu yankuna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar kamfanin dillancin labaran WAFA. Dakarun na Isra'ila sun tafi da Falasɗinawa shida a yankin Ramallah da al Bireh, a cewar kamfanin labaran. Kazalika sun tafi da Falasɗinawa huɗu daga Jenin, ciki har da ƙananan yara biyu, kana sun ɗauke mutane uku a yankin Qalqiliya. Ƙarin labarai ???? 0248 GMT — Lebanon ta gano gawawwakin mutane 23 bayan dakarun Isra'ila sun janye daga kudancin ƙasar Rundunar tsaron fararen-hula ta Lebanon ta ce ta gano gawawwakin mutane 23 a wasu garuruwa da ke kudancin ƙasar bayan dakarun Isra'ila sun janye daga yakunan sakamakon yarjejniyar tsagaita wuta da aka amince da ita. A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce tawagarta da ke kai ɗauki, wadda ke aiki da dakarun rundunar sojin Lebanon, ta gudanar da bincike a yankunan da lIsra'ila ta kai was hare-hare inda ta gano gawawwakin mutanen. Tawagar ta ce ta gano gawawwakin mutum 14 a garin Meiss El Jabal, da gawwaki uku a garin Markaba, da gawawwaki uku a Kfarkela da kuma gawawwaki uku a Odaisseh.