Reshen Hamas masu dauke da makamai, Al Qassam Brigades, ya ce an kai farmaki kan sojojin Isra'ila a sansanin Jabalia da kuma "dakaru masu tsananin aƙidar kafa ƙasar Ira'ila da ke ɓoye a wani gida." Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, reshen Al Qassam Brigades, ta sanar da cewa, ta kashe sojojin Isra'ila 12 a yankin arewacin Gaza da aka yi wa ƙawanya. "A wani gagarumin farmaki da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Zirin Gaza, mayakan Al-Qassam sun kai hari kan wata buldozar soji ta sojan Isra'ila D9 da harsashin Yassin 105 tare da kai hari kan dakaru masu tsananin aƙidar son kafa ƙasar [Isra'ila] da suka kutsa cikin wani gida dauke suka yi fito na fito da su, ”in ji sanarwar a ranar Laraba. “Isar jami’an ceto wajen ke da wuya sai aka tayar da bama-bamai a kan wata tankar Merkava, kuma bayan yunkurin kwato na’urorin sojojin da aka jibge a kasa, sojojin saman Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a yankin ba tare da tausayi ba, sannan mayakanmu sun yi ta luguden wuta. Ya tabbatar da kashe sojojin Isra'ila akalla 12 a farmakin," in ji sanarwar. Tun da farko a ranar Larabar da ta gabata ce sojojin Isra'ila suka sanar da cewa, sun kaddamar da wani gagarumin farmakin soji a tsakiyar sansanin Jabalia, a daidai lokacin da ake ci gaba da kai wani farmaki a gabashin birnin Rafah da ke kudancin Gaza. Ta ce a harin da aka kai a Jabalia, an yi ta gwabza kazamin fadace-fadace, wanda ke nuni da cewa dakarunta "sun yi arangama da tarin mayaƙa," wanda ke nufin wasu ɓangarorin Falasdinawa.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Hamas ta ce mayaƙanta sun kashe sojojin Isra’ila 12 a wani ‘rikitaccen farmaki’
Reshen Hamas masu dauke da makamai, Al Qassam Brigades, ya ce an kai farmaki kan sojojin Isra'ila a sansanin Jabalia da kuma "dakaru masu tsananin aƙidar kafa ƙasar Ira'ila da ke ɓoye a wani gida." Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, reshen Al Qassam Brigades, ta sanar da cewa, ta kashe s...

Reshen Hamas masu dauke da makamai, Al Qassam Brigades, ya ce an kai farmaki kan sojojin Isra'ila a sansanin Jabalia da kuma "dakaru masu tsananin aƙidar kafa ƙasar Ira'ila da ke ɓoye a wani gida." Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, reshen Al Qassam Brigades, ta sanar da cewa, ta kashe s...
