Ankara da Kairo sun jaddada haɗin gwiwarsu wajen goyon bayan Falasɗinu a yayin da ɓangarorin biyu suka sanya hannu kan yarjeniyoyi 17 don ƙarfafa alaƙa a fannoni daban-daban. Turkiyya da Masar suna da buƙatu iri ɗaya kan lamuran da suka shafi Falasɗinawa, kuma dukkansu suna son ganin Isra'ila ta gaggauta daina kai hare-hare a Gaza, a cewar shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan. “Gudunmawar da Turkiyya da Masar suke bayarwa wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tana da matuƙar muhimmanci,” in ji Erdogan ranar Laraba, a yayin da yake gabatar jawabi ga manema labarai tare da takwaransa na ƙasar Masar Abdel Fattah el Sisi, wanda ke ziyarar aiki a Turkiyya. Wannan ce ziyarar aiki ta farko da Sisi ya kai Turkiyya tun da ya soma mulki a 2014. Ya kai ziyarar ce sakamakon gayyatar da Erdogan ya yi masa. A wani ɓangare na ziyarar da Sisi yake yi, shugabannin biyu sun jagoranci wani Babban Taro Kan Haɗin-Kai tsakanin ƙasashen biyu tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi 17 a fannoni daban-daban. "Mun jaddada aniyarmu ta haɗin-kai a dukkan ɓangarori, ciki har da masana'antu da cinikayya da tsaro da kiwon lafiya da muhalli da makamashi,” a cewar Erdogan, wanda ya ƙara da cewa ƙasashen biyu za su kyautata alaƙa a tsakaninsu ta yadda kowane ɓangare zai "ci moriyarta ba.” A nasa ɓangaren, Sisi ya ce ziyarar da ya kai Turkiyya "ta buɗe sabuwar hanya a fannin tattalin arziki da cinikayya,” sannan ya jaddada matsayin ƙasashen biyu game da “wajabcin tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo ƙarshen hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gabar Yammacin Kogin Jordan.”
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Haɗin-kai tsakanin Turkiyya da Masar yana da muhimmanci don samun zaman lafiya da tsaron Gabas ta Tsakiya – Erdogan
Ankara da Kairo sun jaddada haɗin gwiwarsu wajen goyon bayan Falasɗinu a yayin da ɓangarorin biyu suka sanya hannu kan yarjeniyoyi 17 don ƙarfafa alaƙa a fannoni daban-daban. Turkiyya da Masar suna da buƙatu iri ɗaya kan lamuran da suka shafi Falasɗinawa, kuma dukkansu suna son ganin Isra'ila ta...

Ankara da Kairo sun jaddada haɗin gwiwarsu wajen goyon bayan Falasɗinu a yayin da ɓangarorin biyu suka sanya hannu kan yarjeniyoyi 17 don ƙarfafa alaƙa a fannoni daban-daban. Turkiyya da Masar suna da buƙatu iri ɗaya kan lamuran da suka shafi Falasɗinawa, kuma dukkansu suna son ganin Isra'ila ta...
