Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Hadi Sirika: EFCC ta tsare tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Nijeriya

EFCC ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da Sirika tare da ɗan'uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahar N8.06 bn. Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon-ƙasa (EFCC) ta ce ta kama tsohon Ministan Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika bisa zargin almun...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:12
Hadi Sirika: EFCC ta tsare tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Nijeriya
Em resumo

EFCC ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da Sirika tare da ɗan'uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahar N8.06 bn. Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon-ƙasa (EFCC) ta ce ta kama tsohon Ministan Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika bisa zargin almun...

EFCC ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da Sirika tare da ɗan'uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahar N8.06 bn. Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon-ƙasa (EFCC) ta ce ta kama tsohon Ministan Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika bisa zargin almundaha. Shugaban hukumar EFCC Ola Olukoyede ne ya tabbatar da hakan ranar Talata a ganawar da ya yi da manema labarai a Abuja. Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za su gurfanar da Sirika tare da ɗan'uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahar N8.06 bn. Rahotanni sun ce zargin da ake yi wa tsohon ministan yana da alaka da yadda ya tafiyar da batun ƙaddamar da jirgin saman Nijeriya, wato Nigeria Air.