Ana tunanin kwace uranium da aka haɓaka a cibiyoyin nukiliya na Iran Wani rahoto ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump na duba yiwuwar kai harin soji ta ƙasa domin ƙwace tarin uranium da aka haɓaka a Iran. Rahoton ya ce ana kyautata zaton uranium ɗin da aka haɓaka yana ɓoye a ƙarƙashin ƙasa a cibiyar sarrafa nukiliya ta Iran da ke birnin Isfahan. Jami’an sojin Amurka sun ce irin wannan aiki ba zai yiwu da ƙaramin rundunar soji ba, domin zai buƙaci adadi mai yawa na sojojin ƙasa domin kwace kayan nukiliyar cikin tsaro. Masana sun ce irin wannan mataki zai iya zama babbar shigar sojojin ƙasa na Amurka a rikicin, idan har gwamnatin Trump ta yanke shawarar aiwatar da shi. Rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar kimanin kilogram 200 na uranium da aka haɓaka a cibiyar Isfahan, tare da wasu kayayyakin nukiliya da ake kyautata zaton suna cibiyar Natanz. Hukumomin leƙen asirin Amurka sun yi imanin cewa Iran na da hanyoyin shiga karkashin ƙasa da ke ba su damar kaiwa wuraren da aka ɓoye uranium ɗin. A cewar Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, Iran ta riga ta haɓaka uranium zuwa kusan kashi 60 cikin ɗari, matakin da masana ke cewa yana kusa da matakin da ake buƙata domin samar da makaman nukiliya. Sai dai Iran ta dage cewa shirin nukiliyarta na nufin samar da makamashi na zaman lafiya ne kawai, ba domin ƙera makaman nukiliya ba. Shugaba Donald Trump ya sha nanata cewa Amurka ba za ta taɓa barin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba. Tushen labari: Newstimehub
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Rahoto: Gwamnatin Trump na duba yiwuwar kai harin ƙasa a Iran
Ana tunanin kwace uranium da aka haɓaka a cibiyoyin nukiliya na Iran Wani rahoto ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump na duba yiwuwar kai harin soji ta ƙasa domin ƙwace tarin uranium da aka haɓaka a Iran. Rahoton ya ce ana kyautata zaton uranium ɗin da aka haɓaka yana ɓoye a ƙar...

Ana tunanin kwace uranium da aka haɓaka a cibiyoyin nukiliya na Iran Wani rahoto ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump na duba yiwuwar kai harin soji ta ƙasa domin ƙwace tarin uranium da aka haɓaka a Iran. Rahoton ya ce ana kyautata zaton uranium ɗin da aka haɓaka yana ɓoye a ƙar...
