Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Gwamnatin Nijeriya za ta hana kwararar baƙin haure cikin ƙasar daga Agustan 2025

Ministan Harkokin Cikin Gida na Ƙasar ne ya sanar da matakin a ranar Talata a Abuja bayan wata ganawa da ya yi da kungiyar tuntubar ma’aikata ta Nijeriya (NECA). Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta ɗauki matakin hana kwararar baƙin haure cikin ƙasar daga ranar 1 ga watan Agustan 2025, a cewar Ministan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:11
Gwamnatin Nijeriya za ta hana kwararar baƙin haure cikin ƙasar daga Agustan 2025
En bref

Ministan Harkokin Cikin Gida na Ƙasar ne ya sanar da matakin a ranar Talata a Abuja bayan wata ganawa da ya yi da kungiyar tuntubar ma’aikata ta Nijeriya (NECA). Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta ɗauki matakin hana kwararar baƙin haure cikin ƙasar daga ranar 1 ga watan Agustan 2025, a cewar Ministan...

Ministan Harkokin Cikin Gida na Ƙasar ne ya sanar da matakin a ranar Talata a Abuja bayan wata ganawa da ya yi da kungiyar tuntubar ma’aikata ta Nijeriya (NECA). Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta ɗauki matakin hana kwararar baƙin haure cikin ƙasar daga ranar 1 ga watan Agustan 2025, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Ƙasar Olubunmi Tunji-Ojo. Ministan ya sanar da wannan mataki ne a ranar Talata a Abuja bayan wata ganawa da ya yi da ƙungiyar tuntuɓar ma’aikata ta Nijeriya (NECA). Ya ce za a gudanar da “shirin yin afuwa na shige da fice” don daidaita tsare-tsaren wannan mataki a tsawon watanni uku. “Sabon tsarin na hana kwararar baƙin hauren a Nijeriya zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayun 2025,’’ in ji ministan. ‘‘A saboda da haka muka ga dacewar samar da shirin afuwa na shige-da-fice don daidaita ayyukan da kuma tsare-tsaren da suka dace na tsawon watanni uku, wato daga watan Mayu zuwa Yuni, sai daga Yuni zuwa Yuli, sai kuma a ƙarshe daga Yuli zuwa Agusta,” a cewar Tunji. Ministan ya kuma yi gargadin cewa gwamnatin tarayya ba za ta ƙara lamunta da yanayin da wasu kamfanoni ke hana hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyanta ba. "Akan haka, muka ce za mu ƙyale duk wani kamfani da ya ƙi bin wannan tsari ko kuma ya hana Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa gudanar da ayyukanta bisa ga doka ba," in ji Tunji-Ojo.