Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da amincewa da digiri daga Benin da Togo

Ta dauki matakin ne bayan wata jaridar kasar ta wallafa rahoto da ya nuna yadda wakilinta da ya yi bad-da-kama ya samu digiri cikin kasa da wata biyu a wata jami'ar Benin. Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da amincewa da shaidar Digiri na Jami'o'in kasashen Benin da Togo. Ta dauki matakin ne bayan wa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:11
Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da amincewa da digiri daga Benin da Togo
Bu haberde ne var?

Ta dauki matakin ne bayan wata jaridar kasar ta wallafa rahoto da ya nuna yadda wakilinta da ya yi bad-da-kama ya samu digiri cikin kasa da wata biyu a wata jami'ar Benin. Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da amincewa da shaidar Digiri na Jami'o'in kasashen Benin da Togo. Ta dauki matakin ne bayan wa...

Ta dauki matakin ne bayan wata jaridar kasar ta wallafa rahoto da ya nuna yadda wakilinta da ya yi bad-da-kama ya samu digiri cikin kasa da wata biyu a wata jami'ar Benin. Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da amincewa da shaidar Digiri na Jami'o'in kasashen Benin da Togo. Ta dauki matakin ne bayan wata jaridar kasar ta wallafa rahoto da ya nuna yadda wakilinta da ya yi bad-da-kama ya samu digiri cikin wata biyu a Jami'ar Benin. “Wannan rahoton ya tabbatar da zargin da ake yi cewa wasu 'yan Nijeriya suna amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen samun shaidar Didiri domin su samu ayyukan da masu digiri ne suke samu wadanda ba su kamata su samu ba," a cewar wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Ilimi ta Nijeriya Augustina Obilor-Duru ta fitar ranar Talata. Ta kara da cewa “Ma'aikatar Ilimi ta Nijeriya tana yin tir da irin wannan aiki kuma daga ranar 2 ga watan Janairu na 2024 ta dakatar da amincewa da shaidar digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo har sai an kammala binciken da Ma'aikatun Ilimi na Nijeriya da kasashen biyu da kuma Hukumar tsaro ta DSS da Hukumar Kula da Masu yi wa Kasa Hidima, NYSC suke yi.”