Shugaban hukumar da ke sanya ido kan harkokin lantarki ta Nijeriya (NERC), Musliu Oseni ya ce yanzu kwastomomin za su riƙa biyan ₦225 kan kowane kilowat na wuta da suka sha maimakon ₦66 da suke biya a yanzu. Gwamnatin Nijeriya ta ƙara kuɗin wutar lantarki ga rukunin kwastomomin da suka fi samun wuta, waɗanda ake kira Band A customers a turancin Ingilishi. Band A su ne rukunin kwastomomi da suke samun wutar lantarki ta aƙalla awa ashirin a kowace rana. A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ranar Laraba, shugaban hukumar da ke sanya ido kan harkokin lantarki ta Nijeriya (NERC), Musliu Oseni ya ce yanzu kwastomomin za su riƙa biyan ₦225 kan kowane kilowat na wuta da suka sha maimakon ₦66 da suke biya a yanzu. Oseni ya ce waɗannan kwastomomi su ne kashi 15 na mutum miliyan 12 da suke amfani da lantarki a faɗin Nijeriya. Ya ƙara da cewa wannan sabon ƙarin kuɗin lantarki ba zai shafi sauran kwastomomi ba. A watan Janairun da ya gabata, hukumar NERC ta ce gwamnatin Nijeriya za ta kashe kimanin N1.6 tr domin biyan tallafi kan kuɗin lantarki da za a bai wa ƴan ƙasar a shekarar 2024.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Gwamnatin Nijeriya ta ƙara kuɗin lantarki
Shugaban hukumar da ke sanya ido kan harkokin lantarki ta Nijeriya (NERC), Musliu Oseni ya ce yanzu kwastomomin za su riƙa biyan ₦225 kan kowane kilowat na wuta da suka sha maimakon ₦66 da suke biya a yanzu. Gwamnatin Nijeriya ta ƙara kuɗin wutar lantarki ga rukunin kwastomomin da suka fi samun w...