Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Gwamnatin Nijar ta haramta achaɓa a wasu sassan yankin Dosso

Gwamnan yankin Dosso ya ce babban dalilin saka haramcin shi ne daƙile zirga-zirgar ‘yan ta’adda waɗanda suke amfani da babura domin sufuri. Gwamnan yankin Dosso a Jamhuriyar Nijar, Kanal-Manjo Bana Alhassane ya ɗauki mataki mai tsauri a ranar Alhamis inda ya haramta achaɓa da babura a wasu sassan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:11
Gwamnatin Nijar ta haramta achaɓa a wasu sassan yankin Dosso
Kwa muhtasari

Gwamnan yankin Dosso ya ce babban dalilin saka haramcin shi ne daƙile zirga-zirgar ‘yan ta’adda waɗanda suke amfani da babura domin sufuri. Gwamnan yankin Dosso a Jamhuriyar Nijar, Kanal-Manjo Bana Alhassane ya ɗauki mataki mai tsauri a ranar Alhamis inda ya haramta achaɓa da babura a wasu sassan...

Gwamnan yankin Dosso ya ce babban dalilin saka haramcin shi ne daƙile zirga-zirgar ‘yan ta’adda waɗanda suke amfani da babura domin sufuri. Gwamnan yankin Dosso a Jamhuriyar Nijar, Kanal-Manjo Bana Alhassane ya ɗauki mataki mai tsauri a ranar Alhamis inda ya haramta achaɓa da babura a wasu sassan jihar na tsawon watanni uku. Gwamnan ya sanar da saka haramcin ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu inda a wasu sassan ya saka haramcin dindindin na tsawon wata uku, a wasu sassan kuma haramcin zai rinƙa aiki da dare. Gwamnan na Dosso ya ce babban dalilin saka haramcin shi ne daƙile zirga-zirgar ‘yan ta’adda waɗanda suke amfani da babura domin sufuri. Haramcin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun hare-hare na masu iƙirarin jihadi a wasu yankunan ƙasar. Ko a Lahadin da ta gabata, sai da aka kashe sojojin Nijar da dama a wani harin ta’addanci, duk da cewa su ma sojojin sun kashe gomman ‘yan ta’addan. Mutanen da ke zama a karkara da dama sun dogara ne da amfani da babura domin gudanar da sufurinsu inda da wasu ke fargabar saka wannan doka, sai dai gwamnatin ta ce ya zama dole domin daƙile ayyukan ta’addanci.