Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

An Dakatar da Likitoci a Kano Kan Zargin Sakaci da Ya Haddasa Mutuwar Mata Mai Juna Biyu

Gwamnati ta ce bincike ya nuna an bar almakashin tiyata a cikin jikin majiyyaciyar Gwamnatin Jihar Kano a Nijeriya ta dakatar da wasu likitoci da ake zargi da yin sakaci da aikinsu, lamarin da ya haddasa mutuwar wata mata mai juna biyu mai suna Aishatu Umar. Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:11
An Dakatar da Likitoci a Kano Kan Zargin Sakaci da Ya Haddasa Mutuwar Mata Mai Juna Biyu
A taƙaice

Gwamnati ta ce bincike ya nuna an bar almakashin tiyata a cikin jikin majiyyaciyar Gwamnatin Jihar Kano a Nijeriya ta dakatar da wasu likitoci da ake zargi da yin sakaci da aikinsu, lamarin da ya haddasa mutuwar wata mata mai juna biyu mai suna Aishatu Umar. Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kan...

Gwamnati ta ce bincike ya nuna an bar almakashin tiyata a cikin jikin majiyyaciyar Gwamnatin Jihar Kano a Nijeriya ta dakatar da wasu likitoci da ake zargi da yin sakaci da aikinsu, lamarin da ya haddasa mutuwar wata mata mai juna biyu mai suna Aishatu Umar. Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa mutuwar matar, wadda ke da ‘ya’ya biyar, na da alaƙa da sakacin likitoci a Asibitin Kula da Masu Yoyon Fitsari na Abubakar Imam da ke Kano. A cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Suleiman ta fitar, ta ce binciken farko da Sakataren Zartarwa Dakta Mansur Mudi Nagoda ya umarta ya gano cewa an bar almakashin tiyata a cikin jikin majiyyaciyar bayan an yi mata tiyata. Hukumar ta sanar da dakatar da ma’aikata uku da ake zargi da hannu kai-tsaye a lamarin daga ayyukan asibiti nan take, tare da miƙa batun ga Kwamitin Ɗa’a na Lafiya na Jihar Kano domin ƙarin bincike da ɗaukar matakan ladabtarwa. Ta kuma miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar tare da tabbatar wa jama’a cewa ba za ta lamunci duk wani sakaci a cibiyoyin lafiya ba. Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar ta fuskanci matsaloli masu tsanani bayan tiyatar, inda mijinta Abubakar Muhammad ya ce duk da ƙorafin da ta rika yi a asibitin, daga ƙarshe lamarin ya kai ga mutuwarta. Lamarin ya haifar da fushi a tsakanin mazauna Kano tare da ƙara tayar da damuwa kan ingancin kulawar lafiya da ɗaukar alhakin ma’aikata a asibitocin gwamnati, inda mutane da dama ke kira da a yi adalci ga marigayiyar da kuma gyara tsarin kiwon lafiya. Tushen labari: Newstimehub