Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Gwamnatin Ghana ta yi ƙarin kuɗin lantarki da ruwan famfo

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon wasu matsaloli waɗanda suka haɗa da hauhawar farashin dala a ƙasar da tsadar man fetur da gas. Hukumar da ke kula da kamfanonin da ke samar da ababen more rayuwa na Ghana PURC ta sanar da cewa daga Yulin bana, za a yi wa ‘yan ƙasar ƙarin kuɗin lantark...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:11
Gwamnatin Ghana ta yi ƙarin kuɗin lantarki da ruwan famfo
Em resumo

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon wasu matsaloli waɗanda suka haɗa da hauhawar farashin dala a ƙasar da tsadar man fetur da gas. Hukumar da ke kula da kamfanonin da ke samar da ababen more rayuwa na Ghana PURC ta sanar da cewa daga Yulin bana, za a yi wa ‘yan ƙasar ƙarin kuɗin lantark...

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon wasu matsaloli waɗanda suka haɗa da hauhawar farashin dala a ƙasar da tsadar man fetur da gas. Hukumar da ke kula da kamfanonin da ke samar da ababen more rayuwa na Ghana PURC ta sanar da cewa daga Yulin bana, za a yi wa ‘yan ƙasar ƙarin kuɗin lantarki da ruwa. Hukumar ta ce za a yi ƙarin kashi 3.45 cikin 100 ga ƙananan kwastamomi masu amfani da wuta daga kilowatt 0-30, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito. Haka kuma hukumar ta ce ta yi ƙrin kashi 5.84 cikin 100 ga sauran masu gidaje da wuraren kasuwanci masu amfani da wuta daga kilowatt 31 zuwa sama. Ga waɗanda ke a rukunin kamfanoni kuwa, hukumar ta yi musu ƙarin kashi 4.92cikin 100. PURC ta ce duka wannan ƙarin zai soma aiki ne daga ranar 1 ga watan Yulin bana. Ga kuma masu amfani da ruwa, za a samu ƙarin kashi 5.16 ga duka kwastamomi da ke kan kowane rukuni. Ana sa ran wannan ƙarin zai yi aiki tun daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga watan Satumba. Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ƙarin kuɗin lantarkin da na ruwan ne sakamakon wasu matsaloli waɗanda suka haɗa da hauhawar farashin dala a ƙasar da tsadar man fetur da gas.