Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Koma APC a Hukumance

Sauyin jam’iyya ya girgiza siyasar Kano bayan makonni na jita-jita Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma Jam’iyyar APC a hukumance, bayan wani taron karɓarsa da aka gudanar ranar Litinin a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Kano, lamarin da ya kawo ƙarshen makonni na rade-radi kan sauyin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:11
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Koma APC a Hukumance
Кратко

Sauyin jam’iyya ya girgiza siyasar Kano bayan makonni na jita-jita Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma Jam’iyyar APC a hukumance, bayan wani taron karɓarsa da aka gudanar ranar Litinin a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Kano, lamarin da ya kawo ƙarshen makonni na rade-radi kan sauyin...

Sauyin jam’iyya ya girgiza siyasar Kano bayan makonni na jita-jita Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma Jam’iyyar APC a hukumance, bayan wani taron karɓarsa da aka gudanar ranar Litinin a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Kano, lamarin da ya kawo ƙarshen makonni na rade-radi kan sauyin jam’iyyarsa. TRT Hausa Bidiyoyi da suka karade kafafen sada zumunta sun nuna gwamnan tare da manyan jiga-jigan APC na Kano, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Jibrin, tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, Sanata Kawu Sumaila, A.A. Zaura da shugaban APC na jihar Abdullahi Abbas. TRT Hausa Shigar Abba Kabir APC ta zo ne a daidai lokacin da ake ta hasashen ɓaraka tsakaninsa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, lamarin da ya ƙara ɗaga zafin siyasar Kano tare da janyo sauye-sauye a taswirar siyasar jihar. TRT Hausa A jawabinsa, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta ƙara zage damtse wajen aiwatar da ayyuka, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ta matasa ce kuma za a ci gaba da ba su muhimmiyar rawa, tare da alƙawarin ganin canji da haɗin kai da ba a taɓa gani ba a Kano. TRT Hausa Tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Abba Kabir maraba da shiga APC, inda ya bayyana shi a matsayin sabon jagoran jam’iyyar APC a Kano, yayin da Sanata Barau Jibrin ya buƙaci dukkan magoya bayan APC da su mara wa gwamnan baya. TRT Hausa