الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Gwamna Zulum ya haramta sayar da giya a Borno, ya zargi jami’an tsaro da yada mugayen laifuka

Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar. Gwamnan jihar Borno a arewacin Nijeriya, Farfesa Babagana...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:11 ص
Gwamna Zulum ya haramta sayar da giya a Borno, ya zargi jami’an tsaro da yada mugayen laifuka
لمحة سريعة

Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar. Gwamnan jihar Borno a arewacin Nijeriya, Farfesa Babagana...

Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar. Gwamnan jihar Borno a arewacin Nijeriya, Farfesa Babagana Zulum, ya haramta sayar da barasa, yayin da ya zargi sojoji da sauran jami’an tsaro da aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a birnin Maiduguri da kewaye. Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ ayi da k aruwanci da sauran munanan ɗ abi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen kaddamar da wani kwamitin da aka kafa do n “ ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana da maɓoyar miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan dabi’u. “Na yi farin ciki da sanin cewa jami’an soji suna wajen nan, musamman sojoji, ‘yan sanda, da sauran su, domin yawancin wadannan ayyukan wa ke yi n su? W asu daga cikinsu akwai jami’an soji da aka kora da masu ci a yanzu har da farar en hula. "Don haka, bai kamata a ƙi sukar kowane ɓangare ba a cikin wannan lamarin idan har muna son babban birnin Maiduguri da kuma jihar ta kawar da ta'addanci da sauran laifuka," in ji Zulum. A takaitaccen taron, Zulum ya sake kafa kwamitin tare da sake ba wa kwamitin damar kawar da duk wani nau'i na miyagun laifuka da munanan dabi'u a cikin babban birnin Maiduguri da kewaye. D okar hana sayar da barasa da kayan maye, a cewar gwamnan, ta samo asali ne daga yadda ake ta samun tashe-tashen hankula a tsakanin kungiyoyin da ke gaba da juna da kungiyoyin asiri da karuwanci da shaye-shayen miyagun ƙ wayoyi da ‘yan fashi da sata, wadanda suka haddasa asarar rayuka da dukiya. Gwamnan ya hada hannu da sojoji, ‘yan sanda, Civil Defence, da wasu jami’an tsaro da dama da suka hada da civilian JTF domin shiga cikin kwamitin domin gudanar da cikakken bincike. Da yake amincewa da aikin da ke gaban kwamitin da aka sake kafawa, shugaban kwamitin ya yi tir da tabarbarewar harkokin tsaron cikin gida a Maiduguri tare da bayyana matakin da kwamitin zai dauka nan take.