Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Gwamnan Zamfara ya sauya sheƙa zuwa APC

Dauda Lawal ya fice daga PDP sakamakon rikicin cikin gida Gwamnan Jihar Zamfara a Nijeriya, Dauda Lawal, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar, sakamakon rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar. An bayyana matakin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki d...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:11
Gwamnan Zamfara ya sauya sheƙa zuwa APC
Em resumo

Dauda Lawal ya fice daga PDP sakamakon rikicin cikin gida Gwamnan Jihar Zamfara a Nijeriya, Dauda Lawal, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar, sakamakon rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar. An bayyana matakin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki d...

Dauda Lawal ya fice daga PDP sakamakon rikicin cikin gida Gwamnan Jihar Zamfara a Nijeriya, Dauda Lawal, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar, sakamakon rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar. An bayyana matakin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau, inda mataimakin gwamnan jihar, Mani Mummuni, ya wakilci gwamnan wajen sanar da shawarar. Mataimakin gwamnan ya ce an dauki matakin ne bayan shawarwari masu zurfi da kuma nazari kan halin da jam’iyyar PDP ke ciki, musamman dangane da bukatar hadin kai domin magance matsalolin tsaro a jihar. Ya kuma umarci dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke goyon bayan gwamnan da su ajiye mukamansu na PDP, sannan su shirya yin rajista da APC da zarar an bude rajistar sabbin mambobi. Shugabannin siyasar jihar sun kuma bayyana burin kara rajistar sabbin mambobin APC har 400,000 a cikin kwanaki 17 masu zuwa a Zamfara. Matakin ya biyo bayan tuntuba da shawarwari da gwamnan ya fara tun watan Janairu domin duba makomar siyasar jihar yayin da ake shirin babban zaben 2027. Gwamna Lawal ya gode wa jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi na tsayawa takarar gwamna a zaben 2023, tare da cewa duk da sauyin jam’iyya, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin “Rescue Agenda” kamar yadda aka tsara. Tushen labari: Newstimehub