Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Guguwar Hidaya za ta kunna kai Kenya da Tanzania a yayin da ake fama da ambaliyar ruwa

Babban Birnin Kenya na Nairobi na daga yankunan da ake sa ran samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a kwanaki uku masu zuwa, in ji Hukumar Kula da Yanayi ta Kenya. Kenya da Tanzania na shirin fuskantar matsananciyar guguwa a lokacin da ake fuskantar mamakon ruwan sama da mummunar ambaliyar ruwa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:11
Guguwar Hidaya za ta kunna kai Kenya da Tanzania a yayin da ake fama da ambaliyar ruwa
At a glance

Babban Birnin Kenya na Nairobi na daga yankunan da ake sa ran samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a kwanaki uku masu zuwa, in ji Hukumar Kula da Yanayi ta Kenya. Kenya da Tanzania na shirin fuskantar matsananciyar guguwa a lokacin da ake fuskantar mamakon ruwan sama da mummunar ambaliyar ruwa...

Babban Birnin Kenya na Nairobi na daga yankunan da ake sa ran samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a kwanaki uku masu zuwa, in ji Hukumar Kula da Yanayi ta Kenya. Kenya da Tanzania na shirin fuskantar matsananciyar guguwa a lokacin da ake fuskantar mamakon ruwan sama da mummunar ambaliyar ruwa da suka damalmala Gabashin Afirka suka kuma yi ajalin sama da mutum 350 tare da tursasawa dubbai barin matsugunansu. Baya ga janyo asarar rayuka 188 tun watan Maris a Kenya, ambaliyar ruwan ta raba mutum 165,000 da matsugunansu, an samu rahotannin ɓatan mutum 90, in ji Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, inda gwamnati ta gargadi 'yan kasa da su kasance cikin halin kar ta kwana. "Ana bayyana cewa akwai yiwuwar yankin da ke gabar teku ya fuskanci guguwar Hidaya, wadda za ta zo tare da mamakon ruwan sama, guguwa mai ƙarfi da za ta iya shafar harkokin teku a Tekun Indiya," in ji ofishin Shugaban Kasar Kenya William Ruto a ranar Alhamis. A maƙwabciyar Tanzania da akalla mutane 155 suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa, ana sa ran za a fuskanci guguwar ta Hidaya. Mamakon ruwan sama a kwanaki masu zuwa "Zuwa guguwar Hidaya na na iya mamaye dukkan tsarin yanayi a kasar ciki har da mamakon zuwa sama da kakkarfar iska a yankunan da ke gaba da Tekun India," in ji Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross a Tanzania a wata sanarwa ta shafin X. Nairobi babban birnin Kenya na daga cikin yankunan da ake sa ran za su samu mamakon ruwan sama a kwanaki uku masu zuwa, in ji Sashen Kula da Yanayi na Kenya a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na dandalin X, yana mai gargadin yiyuwar samun ƙaƙƙarfar guguwa a gabar tekun kasar. Hukumar hasashen yanayin ta bukaci da a kula sosai saboda yiwuwar samun ambaliya da kwarankwatsa, tana mai kara wa da cewar ƙaƙƙarfar guguwar na iya tumbuke rufin kwanon gidaje da bishiyu da ma sauran barna. Ruwan saman da ba a saba ganin irin sa ba ya janyo ambaliyar da ta yi ajalin mutum 29 da jikkatar wasu 175 a Burundi, wasu dubban kuma sun rasa matsugunansu tun watan Satumban bara, in ji Majalisar Dinkin Duniya. Lamarin ya rutsa da 'yan yawon bude ido A farkon makon nan ne Shugaban Kenya Ruto ya sanar da zai aike da sojoji su kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su. A wata sanarwa da aka fitar a yammacin Alhamis, Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta umarci duk wanda ke zaune a kusa da manyan koguna ko madatsun ruwa da su bar yankunan cikin awanni 24, suna masu gargadin idan ba haka ba to komai zai iya faruwa. Mummunan lamarin ya kuma shafi sashen yawon bude ido na Kenya -- babban sashen habaka tattalin arziki - inda lamarin ya rutsa da 'yan yawon bude ido 100 a Gandun Dajin Maasai Mara a ranar Laraba bayan kogi ya balle, ruwa ya mamaye matsugunan 'yan yawon bude ido. Daga baya masu aikin ceto sun kwashe mutane 90 ta kasa da ta sama, in ji Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida.