Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Gomman mutane sun rasu a harin da sojojin Sudan suka kai kan wani masallaci - Masu fafutuka

Wata ƙungiyar 'yan gwagwarmaya ta bayyana cewa sama da rabin jama'ar da suka rasu a harin da aka kai an kasa gane ko su wane ne. Kwamitin wasu 'yan gwagwarmaya a ranar Talata ya bayyana cewa mutum 31 sun rasu sakamakon wani hari ta sama da sojojin Sudan suka kai a Wad Madani babban birnin Al-Jazi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:11
Gomman mutane sun rasu a harin da sojojin Sudan suka kai kan wani masallaci - Masu fafutuka
Kwa muhtasari

Wata ƙungiyar 'yan gwagwarmaya ta bayyana cewa sama da rabin jama'ar da suka rasu a harin da aka kai an kasa gane ko su wane ne. Kwamitin wasu 'yan gwagwarmaya a ranar Talata ya bayyana cewa mutum 31 sun rasu sakamakon wani hari ta sama da sojojin Sudan suka kai a Wad Madani babban birnin Al-Jazi...

Wata ƙungiyar 'yan gwagwarmaya ta bayyana cewa sama da rabin jama'ar da suka rasu a harin da aka kai an kasa gane ko su wane ne. Kwamitin wasu 'yan gwagwarmaya a ranar Talata ya bayyana cewa mutum 31 sun rasu sakamakon wani hari ta sama da sojojin Sudan suka kai a Wad Madani babban birnin Al-Jazira da ke Sudan kwanaki biyu da suka gabata. An kari harin ne bayan sallar isha'i a ranar Lahadi a birnin da ke kudancin Khartoum kamar yadda Wad Madani Resistance Committee, wadda tana daga cikin ɗaruruwan ƙungiyar da ke bayar da agaji a ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita, kamar yadda wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP ya fitar. Sun zargi sojojin da amfani da "bama-bamai na duro", inda suka ƙara da cewa fiye da rabin wadanda suka mutu har yanzu ba a san ko su waye ba yayin da masu aikin ceto ke tono gawarwakin da aka lalata. Tun a watan Afrilun 2023 ake fafata yaƙi tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar RSF, inda yaƙin ya yi sanadin mutuwar dubban jama'a tare da raba miliyoyin jama'a da muhallansu, wanda adadin shi ne mafi girma a duniya. Duka ɓangarorin biyu sun zargi juna da aikata laifukan yaƙi, daga ciki har da kai hari ba ƙaƙƙautawa kan gidajen farar hula da sace kayayyakin agaji. RSF a nuna yatsa a kanta inda aka zarge ta da sace kayayyaki da yin ƙawanya ga ƙauyaku da cin zarafi ta hanyar lalata a Al-Jazira da kuma tsallaken Sudan.