Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Gomman mutane sun rasu a fashewar tankar mai a hanyar Kaduna zuwa Abuja a Nijeriya

Rahotanni sun ce tankar man ta yi bindiga ne bayan wani ƙaramin hatsari da ta samu, inda jama’ar da ke kusa da wurin suka je kwalfar fetur ɗin da ke cikin tankar. Wata tankar mai wadda ke cike da man fetur ta yi bindiga a ranar Asabar a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:11
Gomman mutane sun rasu a fashewar tankar mai a hanyar Kaduna zuwa Abuja a Nijeriya
A taƙaice

Rahotanni sun ce tankar man ta yi bindiga ne bayan wani ƙaramin hatsari da ta samu, inda jama’ar da ke kusa da wurin suka je kwalfar fetur ɗin da ke cikin tankar. Wata tankar mai wadda ke cike da man fetur ta yi bindiga a ranar Asabar a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a...

Rahotanni sun ce tankar man ta yi bindiga ne bayan wani ƙaramin hatsari da ta samu, inda jama’ar da ke kusa da wurin suka je kwalfar fetur ɗin da ke cikin tankar. Wata tankar mai wadda ke cike da man fetur ta yi bindiga a ranar Asabar a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wanda ke a Jihar Neja. Rahotanni sun ce tankar man ta yi bindiga ne bayan wani ƙaramin hatsari da ta samu, inda jama’ar da ke kusa da wurin suka je kwalfar fetur ɗin da ke cikin tankar. Aƙalla mutum 50 ne suka rasu sakamakon fashewar tankar man, kamar yadda kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta jihar Neja Kumar Tsukwam ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya Gwamnan Jihar Neja Umaru Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa a sanarwar da sakataren watsa labaran Bologi Ibrahim ya fitar. Read More Read More Mummunan hatsarin tankar mai ya jawo asarar rayuka a Jos Ana yawan samun fashewar tankar mai bayan ta yi hatsari a Nijeriya inda jama'a da dama da ke zuwa kwalfar man fetur ke mutuwa. Ko a kwanakin baya sai da fiye da mutum 100 suka rasu a gobarar tankar mai a Jigawa.