'Yan kwana-kwana na ta kokarin kashe gobarar da fashewar gas din ta janyo a unguwar Embakasi da ke Nairobi, inda jami'ai ke cewa akalla mutum biyu sun rasu tare da fargabar cewa za a samu karin mace-mace. An samu gagarumar fashewar a wata cibiyar sayar da gas na girki a Nairobi, babban birnin Kenya inda akalla mutum biyu suka mutu kuma mutum 300 suka jikkata, kamar yadda kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta Kenya da kuma jami'ai suka bayyana. Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da daddare, a cewar ganau. Ana fargabar cewa za a iya samun karin mace-mace. "Ma'aikatan bayar da agajin gaggawa daban-daban sun kubutar da mutum 271 inda aka kai su cibiyoyoin kiwon lafiya da ke Nairobi," kamar yadda kungiyar ba da agaji ta Red Cross a Kenya ta bayyana ranar Juma'a a shafinta na X. Ta kara da cewa an yi wa mutum 27 magani nan-take a wurin da lamarin ya faru. Hotunan bidiyon da aka dauka a unguwar Embakasi sun nuna 'yan kwana-kwana suna kokarin kashe wutan . Wani maimagana da yawun gwamnati ya bayyana cewa ana kokarin cika tukwanen iskar gas ne a lokacin da gobarar ta fara a kusa da karfe sha biyu na dare ranar Alhamis. Shaidu sun bayyana wa kafafen watsa labarai na kasar cewa sun ji mostin kasa bayan fashewar.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Gobara a cibiyar sayar da gas ta kashe mutane, ta jikkata fiye da 300 a Kenya
'Yan kwana-kwana na ta kokarin kashe gobarar da fashewar gas din ta janyo a unguwar Embakasi da ke Nairobi, inda jami'ai ke cewa akalla mutum biyu sun rasu tare da fargabar cewa za a samu karin mace-mace. An samu gagarumar fashewar a wata cibiyar sayar da gas na girki a Nairobi, babban birnin Ken...

Bu haberde ne var?
'Yan kwana-kwana na ta kokarin kashe gobarar da fashewar gas din ta janyo a unguwar Embakasi da ke Nairobi, inda jami'ai ke cewa akalla mutum biyu sun rasu tare da fargabar cewa za a samu karin mace-mace. An samu gagarumar fashewar a wata cibiyar sayar da gas na girki a Nairobi, babban birnin Ken...
