Olanrewaju ya faɗi ne ƙwatsam a lokacin dambe, lamarin da ya sa alƙalin wasa ya nemi taimakon ma’aikatan agaji. Ɗan damben boksin na Nijeriya mai shekara 40, Segun ‘Success’ Olanrewaju, ya mutu bayan ya faɗi a lokacin dambe a Ghana. Tsohon tauraron kambin matsakaicin nauyi na ƙasar yana karawa ne da John Mbanugu a birnin Accra, wanda ake yi wa laƙabi da suna “Power”, a wani ƙaramin dambe a gasar damben boksin ta ƙwararru na Ghana ranar Asabar. “Hukumar damben boksin ɗin Ghana (GBA) ta tabbatar da mutuwar ɗan damben Nijeriya mai suna Gabriel Oluwasegun Olanrewaju a hukumance, wanda ya rasu a asibitin koyarwa na Korle Bu,” in ji wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi. Olanrewaju ya faɗi ƙwatsam a cikin dambe lamarin da ya sa lafari ya nemi taimakon gaggawa. ‘Tsayar da dambe’ “Lafarin, Richard Amevi, da ya lura da yiwuwar haɗari, ya ɗaga hannu don nuna ƙarshen damben kuma nan take ya kira likitan da ke gefen filin dambe da kuma ma’aikatan kiwon lafiya masu taimaka masa daga hukumar lafiya ta gaggawa ta ƙasa domin su taimaka wa ɗan damben wajen farfaɗo da shi,” in ji sanarwar GBA. Wani bidiyon damben da aka wallafa shafukan sada zumunta ya nuna ‘yan damben biyu suna dambe kafin Olanrewaju ya yi tuntuɓe ya faɗi. Ɗan damben Nijeriyan ya daɗe yana damben, inda ya yi damben ƙwararru 23 kuma ya yi nasara a wasanni 13, kuma 12 cikinsu ‘kisa’ (knockout) ya yi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito. Ya sha kaye a wasanni takwas kuma ya yi canjaras a wasanni biyu a tarihin wasanninsa. GBA ta ce hukumar da ke sa ido kan damben boksin a Nijeriya NBBC ta ayyana marigayin a matsayin wanda ke da lafiyar iya wasan dambe kafin hukumar GBA ɗin ta ba da damar wasan na ƙasa da ƙasa. GBA ta ce an sanar da ‘yan sanda lamarin da kuma ma’aikatar wasanni da shaƙatawa ta Ghana.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Ghana ta yi bayani game da mutuwar ɗan damben Nijeriya Olanrewaju
Olanrewaju ya faɗi ne ƙwatsam a lokacin dambe, lamarin da ya sa alƙalin wasa ya nemi taimakon ma’aikatan agaji. Ɗan damben boksin na Nijeriya mai shekara 40, Segun ‘Success’ Olanrewaju, ya mutu bayan ya faɗi a lokacin dambe a Ghana. Tsohon tauraron kambin matsakaicin nauyi na ƙasar yana karawa ne...
Кратко
Olanrewaju ya faɗi ne ƙwatsam a lokacin dambe, lamarin da ya sa alƙalin wasa ya nemi taimakon ma’aikatan agaji. Ɗan damben boksin na Nijeriya mai shekara 40, Segun ‘Success’ Olanrewaju, ya mutu bayan ya faɗi a lokacin dambe a Ghana. Tsohon tauraron kambin matsakaicin nauyi na ƙasar yana karawa ne...
