الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Ghana ta rage kuɗin Aikin Hajji daga GH¢75,000 zuwa GH¢62,000

Kwamitin da Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya kafa kan sake nazarin kuɗin Aikin Hajjin ya ce an rage kuɗin ne domin cika alƙawarin da shugaban ƙasar ya yi na sauƙaƙa wa maniyyata. Kwamitin Aikin Hajji da Shugaba John Dramni Mahama ya sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin bana ya sanar da rage ku...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:11 ص
Ghana ta rage kuɗin Aikin Hajji daga GH¢75,000 zuwa GH¢62,000
لمحة سريعة

Kwamitin da Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya kafa kan sake nazarin kuɗin Aikin Hajjin ya ce an rage kuɗin ne domin cika alƙawarin da shugaban ƙasar ya yi na sauƙaƙa wa maniyyata. Kwamitin Aikin Hajji da Shugaba John Dramni Mahama ya sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin bana ya sanar da rage ku...

Kwamitin da Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya kafa kan sake nazarin kuɗin Aikin Hajjin ya ce an rage kuɗin ne domin cika alƙawarin da shugaban ƙasar ya yi na sauƙaƙa wa maniyyata. Kwamitin Aikin Hajji da Shugaba John Dramni Mahama ya sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin bana ya sanar da rage kuɗin Aikin Hajjin daga GH¢75,000 zuwa GH¢62,000. Kwamitin ya bayyana cewa an rage kuɗin Aikin Hajjin ne domin cika alƙawarin da Shugaba John Dramani Mahama ya ɗauka domin sauƙaƙa wa maniyyata. Haka kuma kwamitin ya bayyana cewa an samu nasarar samun wannan rangwamen ne bayan wata tawaga ta musamman da gwamnatin Ghana ta aika zuwa Saudiyya domin tattaunawa da masu kula da maniyyata domin magance duk wasu matsaloli da maniyyatan ke fuskanta. A yayin da yake magana kan wannan batu, shugaban kwamitin da sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin Alhaji Collins Dauda wanda shi ne ɗan majalisa da ke wakiltar Asutifi South a yankin Ahafo ya jaddada irin kyakkyawan kudiri da shugaban Ghana ke da shi kan sauƙaƙa wa maniyyata ta ɓangaren kashe kuɗi. Read More Read More Shugaba John Mahama ya yi alƙawarin ƙarin hutun Ƙaramar Sallah da rage kuɗin Aikin Hajji ga Musulman Ghana Dama tun a lokacin yaƙin neman zaɓe shugaban na Ghana ya yi alƙawarin sauƙaƙa wa maniyyata. Sannan kwanaki bayan rantsar da shi ya sanar da shirye-shiryen bayar da ƙarin kwana ɗaya a yayin shagulgulan bikin Ƙaramar Sallah da kuma rage kuɗin Aikin Hajji ga Musulman ƙasar.