Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Ghana ta bai wa 'yan asalin Afirka fiye da 500 shaidar zama ɗan ƙasa

Bayar da shaidar zama ɗan ƙasa da Ghanar ta yi na daga cikin wani ɓangare na shirin dawowa da baƙaken-fata da aka ɗauke daga Afirka a lokacin cinikin bayi. Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya yi maraba da 'yan asalin Afirka 524 da ƙasar ta bai wa shaidar zama ɗan ƙasa. Wata sanarwa da ma’aikatar ha...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:11
Ghana ta bai wa 'yan asalin Afirka fiye da 500 shaidar zama ɗan ƙasa
Кратко

Bayar da shaidar zama ɗan ƙasa da Ghanar ta yi na daga cikin wani ɓangare na shirin dawowa da baƙaken-fata da aka ɗauke daga Afirka a lokacin cinikin bayi. Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya yi maraba da 'yan asalin Afirka 524 da ƙasar ta bai wa shaidar zama ɗan ƙasa. Wata sanarwa da ma’aikatar ha...

Bayar da shaidar zama ɗan ƙasa da Ghanar ta yi na daga cikin wani ɓangare na shirin dawowa da baƙaken-fata da aka ɗauke daga Afirka a lokacin cinikin bayi. Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya yi maraba da 'yan asalin Afirka 524 da ƙasar ta bai wa shaidar zama ɗan ƙasa. Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce shugaban ya buƙace su da su haɗa kai su ba da gudunmawarsu ga ci-gaban ƙasar. Sabbin 'yan ƙasar Ghanan sun sha rantsuwar zama 'yan ƙasar ne a yayin wani biki da aka gudanar, wanda hakan wani ɓangare ne na shirin dawowa da baƙaken-fata da aka ɗauke daga Afirka a lokacin cinikin bayi. An ƙaddamar da shirin ne a cikin shekarar 2019, shekara 400 bayan an fara kai 'yan Afirka Amurka a matsayin bayi. Shirin na son ƙara haɗa kan Ghana da tarihinta da kuma ƙara danƙon zumunci tsakaninta da 'yan asalin Afirka da ke ƙasashen ƙetare, in ji sanarwar. A jawabinsa Shugaban Akufo-Addo ya jaddada muhimmancin haɗin-kai da haƙuri da kuma manufofi iri ɗaya. Miliyoyin 'yan Afirka ne dai aka kai nahiyar Amurka a matsayin bayi a lokacin cinikin bayi.