Bayar da shaidar zama ɗan ƙasa da Ghanar ta yi na daga cikin wani ɓangare na shirin dawowa da ɓaƙaken fata da aka dauke daga Afirka a lokacin cinikin bayi. Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya yi maraba da ƴan asalin Afirka 524 da ƙasar ta bai wa shaidar zama ƴan ƙasa. Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce shugaban ya buƙace su da su haɗa kai su ba da gudumawarsu ga ci-gaban ƙasar. Sabbin ƴan ƙasar Ghanan sun sha rantsuwar zama ƴan ƙasar ne a yayin wani biki da aka gudanar, wanda hakan wani ɓangare ne na shirin dawowa da ɓaƙaken fata da aka dauke daga Afirka a lokacin cinikin bayi. An ƙaddamar da shirin ne a cikin shekarar 2019, shekara 400 bayan an fara kai ƴan Afirka Amurka a matsayin bayi. Shirin na son ƙara haɗa kan Ghana da tarihinta da kuma ƙara danƙon zumunci tsakaninta da ƴan asalin Afirka da ke ƙetaren, in ji sanarwar. A jawabinsa Shugaban Akufo-Addo ya jaddada muhimmancin hadin kai da haƙuri da kuma manufofi iri ɗaya. Miliyoyin ƴan Afirka ne dai aka kai nahiyar Amurka a matsayin bayi a lokacin cinikin bayi.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Ghana ta bai wa ƴan asalin Afirka fiye da 500 shaidar zama ɗan ƙasa
Bayar da shaidar zama ɗan ƙasa da Ghanar ta yi na daga cikin wani ɓangare na shirin dawowa da ɓaƙaken fata da aka dauke daga Afirka a lokacin cinikin bayi. Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya yi maraba da ƴan asalin Afirka 524 da ƙasar ta bai wa shaidar zama ƴan ƙasa. Wata sanarwa da ma’aikatar har...

Em resumo