Afirka ta Kudu da Ghana suna da yarjeniyoyin kasuwanci da suka ƙunshi fannonin haɗin-kan tattalin arziƙi, da ƙwarewa, da zamantakewar al'umma, da al'adu. Ghana da Afirka ta Kudu sun amince su faɗaɗa dangantakar kasuwanci da zuba jari ƙarƙashin Yarjejeniyar Cinikayya Mara Shinge ta Nahiyar Afirka. Hakan na zuwa ne bayan wani taron ƙoli tsakanin shugabannin ƙasashen biyu. Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo sun gudanar da tattaunawar a babban birnin Afirka ta Kudu, Pretoria ranar Talata, domin ɗaukaka daɗaɗɗiyar dangantakarsu. Ranar 31 ga Janairun 2024, Afirka ta Kudu ta aike da kashin farko na kayayyaki zuwa Ghana, da ma sauran ƙasashen Afirka, ƙarƙashin shirin Continental Free Trade Agreement (AfCTA), wanda gwamnatin Afirka ta Kudu ta kira da ‘’muhimmin matakin farko.’’ A wata sanarwar bayan taro, shugabannin ƙasashen sun jaddada buƙatar amfani da hanya ta bai-ɗaya wajen aiwatar da matakan shirin AfCTA, musamman don inganta cinikayyar cikin gida a Afirka. Sanarwar ta nuna cewa, “A wannan ɓangare, shugabannin ƙasashen sun nuna gamsuwarsu kan Zauren Kasuwanci na Ghana da Afirka ta Kudu, wanda ya gudana a gefen taron BNC, don ƙasashen biyu suka haɓaka cinikayyar kasuwanci da inganta kasuwancin cikin gida kamar yadda yarjejeniyar AfCTA ta tanada.” Haɓaka zuba jari An ƙaddamar da taron BNC tsakanin Afirka ta Kudu da Ghana yayin da Shugaba Nana Akufo-Addo ya karɓi baƙuncin Shugaba Ramaphosa a birnin Accra a shekarar 2020. Akwai yajeniyoyi da shirye-shirye 24 tsakanin Afirka ta Kudu da Ghana waɗanda suka ƙunshi fannonin haɗin-kan tattalin arziƙi, da ƙwarewa, da kimiyya, da zamantakewar al'umma, da al'adu. Sanarwar ta ƙara da cewa, “A Ghana akwai kamfanonin Afirka ta Kudu. Kamfanoninmu sun shirye don faɗaɗa zuba jari a Ghana, kuma suna neman mu yi aiki tare don haɓaka fagen kasuwanci. Muna gayyatar masu zuba jari daga Ghana da su duba damarmaki a ƙasarmu”. Shugaba Ramaphosa ya yi yuni kan cewa kamfanonin Afirka ta Kudu, ciki har da masu yawa a fannin bankuna, sun bayyana sha'awarsu ta duba damarmakin, don dacewa da shirye-shiryen zuba jari na Ghana. “Akwai damar haɗa gwiwa a ɓangaren kayayyaki tsakanin ƙasashenmu, musamman wajen gina tashoshin safarar kaya, da hanyoyin dogo, da filayen jirgin sama, da asibitoci. Kuma akwai wasu damarmakin a ɓangaren sinadarai. Shugaba Ramaphosa ya ce, “Da yake ƙasashenmu suna da iyakokin ruwa, akwai damar safara ta ruwa tsakaninmu, da wasu damarmakin da ya kamata a duba a wannan ɓangare. Muna buƙatar aiki tare don hana raguwar cinikayya tsakanin ƙasashenmu da muka gani a shekaru huɗu da suka gabata”.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Ghana da Afirka ta Kudu za su faɗaɗa shirin kasuwancin Afirka
Afirka ta Kudu da Ghana suna da yarjeniyoyin kasuwanci da suka ƙunshi fannonin haɗin-kan tattalin arziƙi, da ƙwarewa, da zamantakewar al'umma, da al'adu. Ghana da Afirka ta Kudu sun amince su faɗaɗa dangantakar kasuwanci da zuba jari ƙarƙashin Yarjejeniyar Cinikayya Mara Shinge ta Nahiyar Afirka....

At a glance
Afirka ta Kudu da Ghana suna da yarjeniyoyin kasuwanci da suka ƙunshi fannonin haɗin-kan tattalin arziƙi, da ƙwarewa, da zamantakewar al'umma, da al'adu. Ghana da Afirka ta Kudu sun amince su faɗaɗa dangantakar kasuwanci da zuba jari ƙarƙashin Yarjejeniyar Cinikayya Mara Shinge ta Nahiyar Afirka....
