Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Galatasaray Ta Lallasa Juventus 5-2 A Gasar Zakarun Turai

Ƙungiyar Turkiyya ta yi anfani da katin ja da Juventus ta samu Ƙungiyar Galatasaray ta samu gagarumar nasara da ci 5-2 a kan Juventus wadda ta kammala wasan da ‘yan wasa 10, a zagaye na farko na karawarsu a gasar UEFA Champions League . Noa Lang da Gabriel Sara ne suka fi daukar hankali a wasan....

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:11
Galatasaray Ta Lallasa Juventus 5-2 A Gasar Zakarun Turai
A taƙaice

Ƙungiyar Turkiyya ta yi anfani da katin ja da Juventus ta samu Ƙungiyar Galatasaray ta samu gagarumar nasara da ci 5-2 a kan Juventus wadda ta kammala wasan da ‘yan wasa 10, a zagaye na farko na karawarsu a gasar UEFA Champions League . Noa Lang da Gabriel Sara ne suka fi daukar hankali a wasan....

Ƙungiyar Turkiyya ta yi anfani da katin ja da Juventus ta samu Ƙungiyar Galatasaray ta samu gagarumar nasara da ci 5-2 a kan Juventus wadda ta kammala wasan da ‘yan wasa 10, a zagaye na farko na karawarsu a gasar UEFA Champions League . Noa Lang da Gabriel Sara ne suka fi daukar hankali a wasan. TRT Hausa Gabriel Sara ne ya fara zura ƙwallo a ragar Juventus a minti na 15 da fara wasa, amma Teun Koopmeiners ya rama wa ƙungiyar Italiya nan take. Daga bisani Koopmeiners ya sake zura ƙwallo ta biyu a minti na 32, inda Juventus ta shiga gaba kafin hutun rabin lokaci. TRT Hausa Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Galatasaray ta dawo wasan da ƙarfi, inda Noa Lang ya rama ƙwallo bayan ƙoƙarin Baris Alper Yilmaz. Daga nan Davinson Sanchez ya ƙara wata ƙwallo bayan kwallo da Sara ya turo masa. TRT Hausa A minti na 67, Juventus ta rage zuwa ‘yan wasa 10 bayan da Juan Cabal ya samu katin ja sakamakon katin gargadi biyu. Wannan ya bai wa Galatasaray damar mamaye wasan. TRT Hausa Noa Lang ya sake zura ƙwallo a minti na 75, kafin Sacha Boey ya ƙara ƙwallo ta biyar minti huɗu kafin a tashi daga wasan, inda Galatasaray ta kammala da gagarumar nasara. TRT Hausa Za a buga zagaye na biyu na wasan a birnin Turin ranar 25 ga watan Fabrairu. TRT Hausa