IOM ta ce hare-hare da rashin tsaro na ci gaba da ƙara yawan ‘yan gudun hijira Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa akalla mutane 1,565 ne suka rasa matsugunansu a jihohin Kordofan ta Arewa da ta Kudu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, hukumar ta ce ƙungiyoyinta da ke aiki ƙarƙashin shirin Displacement Tracking Matrix sun gano cewa mutane 1,205 sun tsere daga biranen Bara da Umm Ruwaba da ke Jihar Kordofan ta Arewa. Daga cikin adadin, mutane 580 sun bar Bara yayin da 625 suka tsere daga Umm Ruwaba. Hukumar ta ce ‘yan gudun hijirar sun bazu zuwa wurare daban-daban a Arewacin Kordofan da kuma wasu garuruwa a Jihar White Nile da ke kudancin Sudan. IOM ta kara da cewa sabon adadin ya biyo bayan hare-haren da suka faru a baya, inda mutane 36,625 suka rasa matsugunansu tsakanin ranar 26 zuwa 31 ga Oktoba a Arewacin Kordofan. A wani rahoto na daban, hukumar ta ce mutane 360 sun rasa matsugunansu a Jihar Kordofan ta Kudu, ciki har da 180 daga Al-Abbasiya da 180 daga Delami, waɗanda suka koma wasu yankuna a jihar da kuma garin Tandalti a Jihar White Nile. A halin da ake ciki, hukumomin Sudan sun ce an samu asarar rayuka sakamakon hare-haren jiragen sama marasa matuki da aka kai yankin Zareba al-Sheikh al-Burai a Arewacin Kordofan. A wani ɓangare kuma, ƙungiyar likitoci ta Sudan ta zargi dakarun Rapid Support Forces (RSF) da kashe fararen hula 38 a garin Umm Dam Haj Ahmed. Rahotanni sun ce wani sabon hari da aka kai a yankin ya raba kusan mutane 1,850 da matsugunansu. Rikicin tsakanin Sojojin Sudan da RSF ya fara ne tun ranar 15 ga Afrilu 2023, kuma kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane 20,000 tare da tilasta wa sama da miliyan 15 barin gidajensu, a cewar rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi na cikin gida. Tushen labari: Newstimehub
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Rikicin Sudan ya tilasta wa sama da mutum 1,500 barin gidajensu a Kordofan
IOM ta ce hare-hare da rashin tsaro na ci gaba da ƙara yawan ‘yan gudun hijira Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa akalla mutane 1,565 ne suka rasa matsugunansu a jihohin Kordofan ta Arewa da ta Kudu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro. A cikin wata sanarwa da ta fi...

Кратко
IOM ta ce hare-hare da rashin tsaro na ci gaba da ƙara yawan ‘yan gudun hijira Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa akalla mutane 1,565 ne suka rasa matsugunansu a jihohin Kordofan ta Arewa da ta Kudu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro. A cikin wata sanarwa da ta fi...
