Ousmane Sonko na son Senegal ta shiga cikin masu ƙara a shari'ar da Afirka Ta Kudu ke yi da Isra'ila a Kotun Duniya da ke Hague. Firaministan Senegal Ousmane Sonko ya yi kira da a goyi bayan Falasɗinawa, yana mai tir da abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da kisan kiyashi da ake yi wa Falasɗinawa a Gaza. Da yake jawabi ga wani gangamin siyasa da ɗaruruwan matasa suka halarta a babban birnin ƙasar, Daka, Sonko ya zargi manyan ƙasashen duniya da hannu a masifar da aka kwashe wata takwas ana gani ta mutuwa da rusa abubuwa a Gaza. A kiran da ya yi na kai-tsaye ga Shugaban Senegal Bassirou Diomaye faye, Sonko ya ambato buƙatar Senegal ta goyi bayan ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra'ila a Kotun Duniya da ke Hukunta Masu Laifukan Yaƙi (ICJ) "Zan fara bayanina da kiran jama'a su yi addu'ar sa'a guda ga mutane Falasɗinawa da suka yi shahada...mutanen da a yau ake musu kisan kiyashi da haɗin bakin manyan ƙasashe na wannan duniya," a cewarsa. 'Manyan masu hannu a kisan kiyashi' "Waɗanda suka ayyana kansu a matsayin manyan 'yan dimokraɗiyya, da waɗanda suke kare haƙƙin ɗan adam, su ne a yau manyan masu hannu a kisan kiyashin da ake yi wa Falasɗinawa." A Disambar bara ne, Afrika ta kudu ta shigar da ƙarar Isra'ila tana zarginta da yi wa Falasɗinawa kisan kiyashi a Gaza. Fiye da ƙasashe12 ne suka shiga ko kuma suka bayyana aniyarsu ta shiga cikin masu ƙarar Isra'ila kan kisan kiyashi. Isra'ila ta ci gaba da kai miyagun hare-hare a Gaza tun bayan harin 7 ga watan Oktoba da ƙungiyar Hamas ta kai, duk da ƙudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na tsagaita wuta nan take.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Firaministan Senegal ya yi kira da a goya wa Falasɗinawa baya
Ousmane Sonko na son Senegal ta shiga cikin masu ƙara a shari'ar da Afirka Ta Kudu ke yi da Isra'ila a Kotun Duniya da ke Hague. Firaministan Senegal Ousmane Sonko ya yi kira da a goyi bayan Falasɗinawa, yana mai tir da abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da kisan kiyashi da ake yi wa Falasɗina...

Ousmane Sonko na son Senegal ta shiga cikin masu ƙara a shari'ar da Afirka Ta Kudu ke yi da Isra'ila a Kotun Duniya da ke Hague. Firaministan Senegal Ousmane Sonko ya yi kira da a goyi bayan Falasɗinawa, yana mai tir da abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da kisan kiyashi da ake yi wa Falasɗina...
