الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Fim ɗin 'Water and Garri' na Tiwa Savage na samun shuhura

Tiwa Savage ta fitar da sako ta shafin X tana murnar nasarar da fim din ke samu. Mawakiyar Nijeriya Tiwa Savage ta ce sabon fim ɗin da ta shirya, 'Water and Garri' na samun karbuwa sosai a kasashe 14 na Afirka da wajen nahiyar. Tiwa, wadda cikakken sunanta shi ne Tiwatope Omolara Savage, ta fitar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:11 ص
Fim ɗin 'Water and Garri' na Tiwa Savage na samun shuhura
لمحة سريعة

Tiwa Savage ta fitar da sako ta shafin X tana murnar nasarar da fim din ke samu. Mawakiyar Nijeriya Tiwa Savage ta ce sabon fim ɗin da ta shirya, 'Water and Garri' na samun karbuwa sosai a kasashe 14 na Afirka da wajen nahiyar. Tiwa, wadda cikakken sunanta shi ne Tiwatope Omolara Savage, ta fitar...

Tiwa Savage ta fitar da sako ta shafin X tana murnar nasarar da fim din ke samu. Mawakiyar Nijeriya Tiwa Savage ta ce sabon fim ɗin da ta shirya, 'Water and Garri' na samun karbuwa sosai a kasashe 14 na Afirka da wajen nahiyar. Tiwa, wadda cikakken sunanta shi ne Tiwatope Omolara Savage, ta fitar da sakon yin murna a shafin X don murnar nasarar shoirin fim din ta, wanda ake kallo a manhajar Prime Video. "Yana kan gaba a kasashe 14. Gidiya ga ahalin WAG (Water And Garri) a duk fadin duniya bisakauna da goyon bayan da suka nuna," in ji Savage a sakon nata. Shirin fim din Water And Garri da Savage ta shirya tare da mai shirya fina-finai a Nijeriya Jimi Adesanya, ya fara fita ta manhajar Prime Video a ranar Juma'a, 10 ga Mayu, 2024. A fadin Tiwa Savage "Water And Garri na ta samun karbuwar masu kallo a Nijeriya, Ghana, Kamaru, Benin, Rwanda, Togo, Zmabia, Cyprus, Uganda, Ukraine, Tanzania, Qatar da Afirka ta Kudu. Shirin fim din na bayar da labarin Aisha (Savage da kanta ce ta fito a matsayin ta), mai sana'ar dinki da ke da burin dawo wa kauyensu bayan shafe tsawon shekaru a Amurka. Ammma bayan zuwan ta sai Aisha ta gano cewar wajen da a baya take kira gida a yanzu cike yake da rikici da tashin hankali. An dauki shirin fim din da Meji Alabi ya bayar da umarni a Cape Coast, Ghana, kuma ya kunshi jarumai irin su Mike Afolarin, Andrew Bunting da Jemima Osunde.