Manchester United ta rasa matsayinta na farko a duniya, a yawan masu shiga kallon kwallo a filin wasanta a shekarar 2023. Haka kuma an doke Arsenal daga jerin kungiyoyi goma mafi farin-jinin 'yan kallo. A shekarar 2023, filin wasan kwallon kafa da aka shiga don kallon kwallo a duniya shi ne Camp Nou, wato filin wasa na Barcelona, inda 'yan kallo 83,273 suke shiga kallo duk wasan Barca na gida, bisa matsakaicin adadi. Filayen wasan kwallon kafa 16 a duniya da suka fi tara 'yan kallo, duka suna nahiyar Turai ne. Uku suna Jamus sannan uku suna birnin Landan shi kadai. Kasar da ta fi yawan kungiyoyin kwallo a jerin ita ce Jamus wadda take da kulob 12 da ke buga wasa a matakan kwararru biyu na kasar. Wadda ke biye mata ita ce Ingila, da kulob 11, sai Sifaniya mai kulob 7 da Italiya mai kulob 6. A kididdigar kasashe 14 suka shiga jerin manyan filayen wasa a yawan masu kallo. Babban kulob da ke kan-gaba amma wanda ke wajen Turai shi ne filin wasa na kungiyar Flamengo ta Brazil, wadda take mataki na 17 a duniya, kuma take da adadin 'yan kallo 56,689 duk wasa a shekarar ta 2023. Shafin Transfer Markt ya wallafa wannan kididdiga da ta nuna cewa a nahiyar Arewacin Amurka kungiyar Atlanta United tana da 'yan kallo 47,526 a wasanninta na gida, wanda ya ba ta mataki na 30 a jerin. Kasar Sifaniya tana da filaye bakwai da ke cikin jerin, amma kulob shida ne ka da filayen. Wannan ya faru ne saboda Bercalona ta shafe rabin shekara tana buga wasa a filin ta na Camp Nou, yayin da sauran ta buga wasanni a babban filin wasan Olympic lokacin da ake gyare-gyare a gidanta. A Asiya kuwa kulob din kasar China mai suna Bejing Guoan bayan da suka sami 'yan kallo 43,769 duk wasansu na gida.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Filayen kwallo aka fi shiga a duniya a shekarar 2023
Manchester United ta rasa matsayinta na farko a duniya, a yawan masu shiga kallon kwallo a filin wasanta a shekarar 2023. Haka kuma an doke Arsenal daga jerin kungiyoyi goma mafi farin-jinin 'yan kallo. A shekarar 2023, filin wasan kwallon kafa da aka shiga don kallon kwallo a duniya shi ne Camp...

Em resumo
Manchester United ta rasa matsayinta na farko a duniya, a yawan masu shiga kallon kwallo a filin wasanta a shekarar 2023. Haka kuma an doke Arsenal daga jerin kungiyoyi goma mafi farin-jinin 'yan kallo. A shekarar 2023, filin wasan kwallon kafa da aka shiga don kallon kwallo a duniya shi ne Camp...
