Jirgin saman Max Air ƙirar 737 ɗauke da fasinjoji 59 ya zame daga kan titinsa a filin jirgin saman Mallam Amini da ke Kano bayan tayarsa ta fashe. Fasinjoji 59 daga birnin Legas zuwa Kano sun tsallake rijiya da baya bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa a birnin Kano inda ya zame daga kan titin jirgi bayan tayarsa ta fashe. Kamfanin dillancin labaran Turkiyya (AA) ya ambato wasu fasinjojin jirgin suna cewa jirgin ya rasa ɗaya daga cikin ababen saukarsa ne a lokacin da ya zo sauka ranar Talata da daddare. Manajan Kamfanin Max Air a Kano, Bello Ramadan ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce babu wanda ya rasu a cikin matafiyan. Filayen jiragen saman Nijeriya uku ne kaɗai suke samar da kuɗaɗen-shiga - FAAN Kuma kamfanin jiragen saman Max Air ya ce za a rufe titin jirgin saman filin saukar jirgi na Mallam Aminu Kano na wucin-gadi zuwa lokacin da aka kammala bincike kan lamarin. Lamarin dai ya faru da misalin ƙarfe 10.57 na dare a lokacin da jirgin ya isa filin jirgin saman Mallam Aminu Kano daga filin jirgin Murtala Mohammed na Legas.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Fasinjoji 59 sun tsira bayan tayar jirgin Max Air ta fashe a Kano
Jirgin saman Max Air ƙirar 737 ɗauke da fasinjoji 59 ya zame daga kan titinsa a filin jirgin saman Mallam Amini da ke Kano bayan tayarsa ta fashe. Fasinjoji 59 daga birnin Legas zuwa Kano sun tsallake rijiya da baya bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa a birnin Kano inda ya zame daga kan titin jir...