Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Faransa ta rufe ofishin jakadancinta na Nijar har 'sai abin da hali ya yi'

Rufe ofishin jakadancin dai a halin yanzu na daga cikin alamomin karshe wadanda ke nuna cewa Faransa ta kammala tattara kayanta daga kasar da ta yi wa mulkin mallaka. Faransa ta rufe ofishin jakandacinta na Nijar har sai abin da hali ya yi, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Faransar ta tabbat...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:10
Faransa ta rufe ofishin jakadancinta na Nijar har 'sai abin da hali ya yi'
De un vistazo

Rufe ofishin jakadancin dai a halin yanzu na daga cikin alamomin karshe wadanda ke nuna cewa Faransa ta kammala tattara kayanta daga kasar da ta yi wa mulkin mallaka. Faransa ta rufe ofishin jakandacinta na Nijar har sai abin da hali ya yi, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Faransar ta tabbat...

Rufe ofishin jakadancin dai a halin yanzu na daga cikin alamomin karshe wadanda ke nuna cewa Faransa ta kammala tattara kayanta daga kasar da ta yi wa mulkin mallaka. Faransa ta rufe ofishin jakandacinta na Nijar har sai abin da hali ya yi, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Faransar ta tabbatar a ranar Talata. Sanarwar na zuwa ne kusan mako biyu bayan rukunin karshe na sojojin Faransar ya bar Jamhuriyar Nijar. Rufe ofishin jakadancin dai a halin yanzu na daga cikin alamomin karshe wadanda ke nuna cewa Faransa ta kammala tattara kayanta daga kasar da ta yi wa mulkin mallaka. A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar ta ce "A yanzu haka ofishin jakadancin Faransa a Nijar ya rufe har sai abin da hali ya yi." Duka wadannan sun biyo bayan juyin mulkin da sojojin na Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023. Ta ce tsawon watanni biyar tun bayan juyin mulkin "Ofishin Jakadancinmu ya fuskanci cikas sosai wanda ya sa ba zai iya gudanar da ayyukansa ba" ciki har da shingen da ke kewaye da ofishin. Tafiyar sojojin Faransa Akasarin jami’an ofishin jakadancin, daga ciki har da jakadan kasar sun bar kasar a kwanakin baya tun bayan da gwamnatin sojin kasar ta sallame su. Rukunin sojojin Faransa mai dakaru 1,500 ya bar Nijar a ranar 22 ga watan Disambar 2023. Sojojin kasar sun hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, tare da watsi da duk wasu yarjejeniyoyi da Faransar ta yi da Nijar. Har yanzu Bazoum na karkashin daurin talala a Yamai tun bayan yi masa juyin mulki