Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Faransa ta miƙa sansanin sojinta ɗaya tilo da ke Ivory Coast

Faransa a ranar Alhamis ta janye daga sansani ɗaya da take da shi a ƙasar Ivory Coast da ke Yammacin Afirka, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito. Faransa a ranar Alhamis ta janye daga sansani ɗaya da take da shi a ƙasar Ivory Coast da ke Yammacin Afirka, kamar yadda kafafen watsa labar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:10
Faransa ta miƙa sansanin sojinta ɗaya tilo da ke Ivory Coast
De un vistazo

Faransa a ranar Alhamis ta janye daga sansani ɗaya da take da shi a ƙasar Ivory Coast da ke Yammacin Afirka, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito. Faransa a ranar Alhamis ta janye daga sansani ɗaya da take da shi a ƙasar Ivory Coast da ke Yammacin Afirka, kamar yadda kafafen watsa labar...

Faransa a ranar Alhamis ta janye daga sansani ɗaya da take da shi a ƙasar Ivory Coast da ke Yammacin Afirka, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito. Faransa a ranar Alhamis ta janye daga sansani ɗaya da take da shi a ƙasar Ivory Coast da ke Yammacin Afirka, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito. Ministan Tsaron Fatansa Sebastien Lecornu a hukumance ya halarci bikin rufe sansanin. Ivory Coast ko kuma Côte d'Ivoire, ƙasa ce da a baya ke ƙarƙashin ikon Faransa. A halin yanzu za ta ci gaba da haɗa kai da Faransa ta ɓangaren aikin soji, kamar yadda a baya Ministan Tsaron Ivory Coast Tene Birahima Ouattara ya sanar. Sansanin da ke Port-Bouet wanda ke a kusa da babban birnin ƙasar Abidjan, za a mayar da sunansa sansanin Thomas d'Aquin Ouattara, wato sunan shugaban sojin ƙasar na farko. Raguwar tasirin Faransa Sojojin Faransa a nahiyar Afirka na ci gaba da raguwa a 'yan shekarun nan bayan da kasashen yankin da suka hada da Chadi da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso suka fatattaki sojojin da suka yi wa ƙasashen mulkin mallaka a baya. A halin yanzu dai sojojin Faransa na ci gaba da zama a kasashen Djibouti da Gabon, kasashen biyu da ba su nuna sauye-sauye ga yarjejeniyoyin da suka kulla da Paris kan kasancewar sojojinta ba.