الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Falasdinwa sun koma cin abincin dabbobi saboda yadda yakin Isra'ila ya jawo yunwa a Gaza

Maudu'in #GazaStarving na ci gaba da yaduwa a kafafen sada zumunta na zamani don nuna yunwar da ke kunno kai a Gaza sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa. Yayin da halin da Falasdinawan ke ciki a Gaza ke kara ta'azzara a kowace rana a karkashin munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:10 ص
Falasdinwa sun koma cin abincin dabbobi saboda yadda yakin Isra'ila ya jawo yunwa a Gaza
لمحة سريعة

Maudu'in #GazaStarving na ci gaba da yaduwa a kafafen sada zumunta na zamani don nuna yunwar da ke kunno kai a Gaza sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa. Yayin da halin da Falasdinawan ke ciki a Gaza ke kara ta'azzara a kowace rana a karkashin munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa...

Maudu'in #GazaStarving na ci gaba da yaduwa a kafafen sada zumunta na zamani don nuna yunwar da ke kunno kai a Gaza sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa. Yayin da halin da Falasdinawan ke ciki a Gaza ke kara ta'azzara a kowace rana a karkashin munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa, maudu'in #GazaStarving na ci gaba da yaduwa a shafukan sada zumunta inda aka nuna bidiyon da ke nuna mutane masu fama da yunwa suna cin abincin dabbobi, yayin da su kuma dabbobin suke cin gawarwakin mutane da ke yashe a kan tituna. A cikin 'yan kwanaki kadan kawai, an yi amfani da maudu'in #GazaStarving - sau kusan miliyan biyar a shafin X, yayin da a sauran shafukan sada zumunta, ciki har da Instagram da TikTok, ake amfani da maudu'in don bayyana yunwar da Falasdinawa ke fuskanta. Tashen da maudu'in #GazaStarving ke yi ya fito da ainihin fargabar yunwa da ake fama da ita a Gaza, yayin da rahotanni suka fara bayyana a shafukan sada zumunta na yadda Falasdinawa ke niƙa abincin dabbobi saboda ƙarancin alkama da burodi. Bidiyo da dama sun nuna Falasdinawa da ke fama da yunwa suna cin abincin dabbobi, yayin da kyanwowi da karnuka suka mayar da gawarwakin mutanen da ke yashe a kan titi abincinsu. Sojojin Isra'ila na ci gaba da aiwatar da munanan ayyukan da suke yi, tare da nuna ƙyama ga gawarwakin Falasdinawan da ba a binne ba a kudancin birnin Khan Younis, tare da hana jama'a tattara su daga ɓaraguzan gine-gine, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa Anadolu a ranar Laraba. Shaidun gani da ido sun ce wasu Falasdinawa sun koma yankunan da sojojin Isra'ila suka janye domin gano gawarwakin 'yan'uwansu da suka haɗa da yara da mata, waɗanda tankokin yakin Isra'ila suka kai musu hari a yayin da suke yunkurin tserewa daga birnin Khan Younis zuwa Rafah mai nisa daga. Burodin da aka yi da abincin dabbobi Sun ce motocin daukar marasa lafiya sun yi jigilar wasu gawarwakin zuwa cibiyar kula da lafiya ta Nasser da ke tsakiyar birnin, amma lokacin da tankunan Isra’ila suka bude wuta kan kowa da kowa a yankin, sai da jami’an agajin suka gudu. Wasu daga cikin gawarwakin sun fara ruɓewa, kuma wasu kyanwowi da karnuka sun cinye sassan jikinsu, in ji su. Hotunan bidiyo da dama da suka yi amfani da maudu'in sun nuna Falasdinawa suna cin biredin da aka yi da abincin dabbobi. A cewar wani wakilin Anadolu a arewacin Gaza, an lura cewa mutane suna sayen abincin dabbobi a kasuwannin arewacin Gaza a matsayin abincinsu, saboda yadda fulawa da alkama suka yi ƙaranci. Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutum miliyan 2.2 a Gaza, karkashin hare-haren Isra'ila, na fuskantar barazanar yunwa. Yayin da Isra'ila ke barin wasu motocin agaji kadan zuwa Gaza, an kuma raba wadannan manyan motocin ne a yankunan kudancin Gaza, yayin da ake ci gaba da hana yankunan arewacin Gaza saboda mamayar Isra'ila. Isra'ila ta kai wani mummunan hari a Zirin Gaza bayan harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, inda ta kashe Falasdinawa akalla 25,700 tare da jikkata 63,740. Kusan ‘yan Isra’ila 1,200 ne ake kyautata zaton an kashe a harin na Hamas.