Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Fafaroma Leo na 14 ya ziyarci Masallacin Sultanahmet da ke Istanbul

Fafaroman ya zagaye masallacin tare da muƙarrabansa, wanda shi ne masallaci na farko na Daular Usmaniyya da ke da hasumiya shida. Shugaban Fadar Vatican, Fafaroma Leo na 14 ya ziyarci Masallacin Sultanahmet a ranar Asabar wanda masallaci ne mai tarihi da ke birnin Istanbul a matsayin wani ɓangare...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:10
Fafaroma Leo na 14 ya ziyarci Masallacin Sultanahmet da ke Istanbul
Kwa muhtasari

Fafaroman ya zagaye masallacin tare da muƙarrabansa, wanda shi ne masallaci na farko na Daular Usmaniyya da ke da hasumiya shida. Shugaban Fadar Vatican, Fafaroma Leo na 14 ya ziyarci Masallacin Sultanahmet a ranar Asabar wanda masallaci ne mai tarihi da ke birnin Istanbul a matsayin wani ɓangare...

Fafaroman ya zagaye masallacin tare da muƙarrabansa, wanda shi ne masallaci na farko na Daular Usmaniyya da ke da hasumiya shida. Shugaban Fadar Vatican, Fafaroma Leo na 14 ya ziyarci Masallacin Sultanahmet a ranar Asabar wanda masallaci ne mai tarihi da ke birnin Istanbul a matsayin wani ɓangare na ziyararsa a hukumance zuwa Turkiyya. Fafaroman ya zagaye masallacin tare da muƙarrabansa, wanda shi ne masallaci na farko na Daular Usmaniyya da ke da hasumiya shida. Ministan Al'adu da Yawon Shaƙatawa na Turkiyya, Mehmet Nuri Ersoy, da babban mai bayar da fatawa na Istanbul Emrullah Tuncel, da ma'aikatan masallacin sun taya shi zagayen masallacin a yayin ziyarar. Muezzin Asgin Musa Tunca ya ba Fafaroma Leo na 14 bayanai kan tsarin gine-ginen masallacin da kuma muhimmancinsa a tarihi. Fafaroma Leo na 14 ya isa Turkiyya a ranar Alhamis wadda ita ce tafiyarsa ta farko a hukumance zuwa ƙasar waje, a gayyatar Shugaba Recep Tayyip Erdoğan. A lokacin da ya isa, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a duniya kuma ya ce yana fatan wannan tafiyar tasa za ta sa duniya ta tabbatar da muhimmancin zaman lafiyar ga duniya. An tarbi Fafaroma a filin jirgin sama na Ankara babban birnin Turkiyya, inda Ministan Al'adu da Yawon Shaƙatawa Mehmet Nuri Ersoy ne ya tarbe sa da wasu jami'ai. Wasu daga cikin jami’an Fadar Vatican da suka yi masa rakiya sun haɗa da Cardinal Pietro Parolin da Archbishop Paul Richard Gallagher.