Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Euro 2024: An tashi 2-2 tsakanin Croatia da Albania

Croatia ta shiga tsaka mai wuya a halin yanzu domin kuwa idan har tana so ta kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale, sai ta yi nasara a wasan da za ta buga da Italiya a ranar 24 ga watan Yuni. An tashi 2-2 a wasan da aka kara tsakanin Albania da Croatia a Gasar Euro 2024 a ranar Laraba. Tashin da aka yi can...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:10
Euro 2024: An tashi 2-2 tsakanin Croatia da Albania
De un vistazo

Croatia ta shiga tsaka mai wuya a halin yanzu domin kuwa idan har tana so ta kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale, sai ta yi nasara a wasan da za ta buga da Italiya a ranar 24 ga watan Yuni. An tashi 2-2 a wasan da aka kara tsakanin Albania da Croatia a Gasar Euro 2024 a ranar Laraba. Tashin da aka yi can...

Croatia ta shiga tsaka mai wuya a halin yanzu domin kuwa idan har tana so ta kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale, sai ta yi nasara a wasan da za ta buga da Italiya a ranar 24 ga watan Yuni. An tashi 2-2 a wasan da aka kara tsakanin Albania da Croatia a Gasar Euro 2024 a ranar Laraba. Tashin da aka yi canjaras ya jefa Croatia cikin hatsari sakamakon za a iya waje da ƙasar a matakin rukuni. Klaus Gjasula ya ci gidansa Albania a bisa kuskure a minti na 76 sai dai a lokutan ƙarshe na tashi wasan ya samu nasarar ci wa ƙasarsa ƙwallo domin wanke laifinsa. Bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Sifaniya da ci 3-0 a wasansu na farko, Croatia na a baya a lokacin da Qazim Laci ya ci wa Albania ƙwallon farko a Hamburg. Sai dai Croatia ta farfaɗo a wasan bayan da ta sauya ‘yan wasa biyu, inda Andrej Kramaric ya rama ƙwallon wanda hakan ya ja suka zama kunnen doki. Bayan minti biyu da haka sai Gjasula ya ci gidansa Albania bisa kuskure. Sai dai ɗan wasan tsakiyar na Albania ya zama gwarzo a ƙarshen wasan ana dab da tashi wanda hakan ya ja suka tashi canjaras. Ƙasar Croatia, wadda ta kai zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Euro 2022, akwai buƙatar ta ci wasan da za ta buga da Italiya a ranar 24 ga watan Yuni idan har tana so ta kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale.