Shugaban Turkiyya ya gargaɗi ƙasashen Kusurwar Afirka kan tsoma bakin ƙasashen waje Shugaban Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya a ranar Talata ya soki matakin Isra’ila na amincewa da Somaliland a matsayin ƙasa mai ’yanci, yana mai cewa wannan mataki ba zai amfani Somaliya ko ma yankin Kusurwar Afirka gaba ɗaya ba. TRT Hausa Erdogan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai tare da Firayiministan Ethiopia , Abiy Ahmed , a Addis Ababa , inda ya jaddada cewa ya kamata ƙasashen yankin su nemo mafita daga cikinsu ba tare da barin yankin ya zama “fagen fafatawar ƙasashen waje” ba. TRT Hausa Shugaban na Turkiyya ya kuma jaddada ƙarfin dangantakar diflomasiyya tsakanin Turkiyya da Habasha, yana mai cewa fiye da kamfanonin Turkiyya 200 da jarin kusan dala biliyan 2.5 suna aiki a Habasha, inda suke samar da ayyukan yi ga kimanin mutane 20,000. TRT Hausa Habasha na neman damar zuwa teku A nasa ɓangaren, Firayiminista Abiy Ahmed ya ce ya nemi goyon bayan Turkiyya kan ƙoƙarin Habasha na samun damar zuwa teku, yana mai bayyana hakan a matsayin muhimmin batu a tattaunawarsa da Erdogan. TRT Hausa Abiy ya ce Habasha, wadda ta zama ƙasa marar bakin teku tun bayan samun ’yancin Eritrea a 1993, na kallon samun hanyar zuwa teku a matsayin muhimmin abu ga dabarun ƙasarta na dogon lokaci. TRT Hausa Shugabannin kasashen biyu sun tattauna faɗaɗa hulɗar kasuwanci, inda aka bayyana burin ƙara ciniki tsakanin Turkiyya da Habasha zuwa aƙalla dala biliyan 1, tare da ƙarfafa ƙarin zuba jari daga kamfanonin Turkiyya musamman a fannonin masana’antu da gine-gine. TRT Hausa Haka kuma bangarorin sun tattauna haɗin gwiwa a matakin duniya, ciki har da batutuwan sauyin yanayi da taron COP31, wanda aka shirya gudanarwa a Turkiyya a shekara mai zuwa sannan kuma a Habasha. TRT Hausa
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Erdogan: Amincewar Isra’ila da Somaliland Ba Za Ta Amfani Yankin Ba
Shugaban Turkiyya ya gargaɗi ƙasashen Kusurwar Afirka kan tsoma bakin ƙasashen waje Shugaban Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya a ranar Talata ya soki matakin Isra’ila na amincewa da Somaliland a matsayin ƙasa mai ’yanci, yana mai cewa wannan mataki ba zai amfani Somaliya ko ma yankin Kusurwar Afir...

لمحة سريعة
Shugaban Turkiyya ya gargaɗi ƙasashen Kusurwar Afirka kan tsoma bakin ƙasashen waje Shugaban Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya a ranar Talata ya soki matakin Isra’ila na amincewa da Somaliland a matsayin ƙasa mai ’yanci, yana mai cewa wannan mataki ba zai amfani Somaliya ko ma yankin Kusurwar Afir...
