Hukumar Kula Da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta bayyana Ennedi Massif a matsayin wani wuri na al'ada da tarihi.. Daga Sylvia Chebet A arewa maso gabashin Chadi, dutsen yashi na Ennedi Massif ya samo asali ne bayan ruwa da zaizayar ƙasa sun samar da shi tsawon lokaci, wanda a cikinsa akwai tuddai da kwari da ƙorama wadda ta ratsa ta ciki Duwatsu masu ban sha'awa da iska da zaizayar ƙasa suka samar sun samar da kyawawan gine-gine. / Hoto: Getty Images Kalmar Ennedi na nufin gida mai kyau a harshen ƙasar. Makiyaya da ke magana da harshen Dazaga suna zaune a yankin. Kuma addinin Musulunci suke bi. Ennedi ya kasance wurin mai ban sha'awa sakamakon yadda sassaƙaƙun gine-gine suke. / Hoto: Getty Images Ennedi na da girman murabba'in kilomita 40,000 kuma shimfidar wurin ta sahara ce. Akwai ruwa a kowane lokaci a kwance a wasu sassa na Ennedi. / Hoto: Getty Images Ennedi ya kasance wurin da yanayi ya haɗu da tarihi. Haka kuma wuri ne da ke da arziƙin al'adu. Akwai namun daji da dama a Ennedi. / Hoto: Getty Images Hukumar Kula Da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta bayyana Ennedi Massif a matsayin wani wuri na al'ada da tarihi. Irin rubutun da ke jikin duwatsun wurin wasu alamu ne na tarihin Ennedi tsawon dubban shekaru. / Hoto: Getty Images Mutanen farko da suka yi zama a wurin sun yi kwaliyya da dubban zane-zane kan duwatsu da cikin koguna wanda hakan ya samar ɗaya daga cikin zane-zane na kimiyya kan duwatsu mafi girma a Sahara.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Ennedi: Wani ɓoyayyen wurin tarihi da ke cikin Saharar Chadi
Hukumar Kula Da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta bayyana Ennedi Massif a matsayin wani wuri na al'ada da tarihi.. Daga Sylvia Chebet A arewa maso gabashin Chadi, dutsen yashi na Ennedi Massif ya samo asali ne bayan ruwa da zaizayar ƙasa sun samar da shi tsawon lokaci, wanda...

Em resumo
Hukumar Kula Da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta bayyana Ennedi Massif a matsayin wani wuri na al'ada da tarihi.. Daga Sylvia Chebet A arewa maso gabashin Chadi, dutsen yashi na Ennedi Massif ya samo asali ne bayan ruwa da zaizayar ƙasa sun samar da shi tsawon lokaci, wanda...
