Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Emine Erdogan da shugaban MDD sun tattauna kan sauyin yanayi da shirinta na Zero Waste

A taron COP29, Azabaijan na shirin jagorantar zaman tattauna kan shirin sauyin yanayi tare da haɗin gwiwar Turkiyya. Uwargidan shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdoğan ta gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterre a hedkwatar Majalisar da ke birnin New York, inda suka ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:10
Emine Erdogan da shugaban MDD sun tattauna kan sauyin yanayi da shirinta na Zero Waste
Kwa muhtasari

A taron COP29, Azabaijan na shirin jagorantar zaman tattauna kan shirin sauyin yanayi tare da haɗin gwiwar Turkiyya. Uwargidan shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdoğan ta gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterre a hedkwatar Majalisar da ke birnin New York, inda suka ta...

A taron COP29, Azabaijan na shirin jagorantar zaman tattauna kan shirin sauyin yanayi tare da haɗin gwiwar Turkiyya. Uwargidan shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdoğan ta gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterre a hedkwatar Majalisar da ke birnin New York, inda suka tattauna kan shirinta na sarrafa shara a duniya wato 'Zero Watse' da kuma batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, kamar yadda wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ta bayyana. A matsayinta na shugabar kwamitin ba da shawarwari kan shirin Zero Watse a MDD, Erdogan ta bayyana ayyukan da hukumar ke yi na ƙudurin samar da ci gaba mai ɗorewa a yayin ganawarta da Guterres a ranar Talata, inda ta jaddada muhimmancin tallafin da MDD ke bayarwa. Kazalika Emine Erdogan ta bayyana irin haɗin gwiwar Turkiyya da Azabaijan a shirye-shiryen taron sauyin yanayi na MDD karo na 29 (COP29), wanda za a gudanar a Baku a cikin watan Nuwamba. Daya daga cikin ranakun jigo a COP29 ana sa ran za a mai da hankali kan "Zero Waste," tare da wasu abubuwan da suka shafi abubuwan da aka tsara a kusa da shirin, in ji Uwargidan Erdogan. Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa, ana sa ran gudanar da taron kai tsaye na kwamitin ba da shawara na MDD karo na uku a COP29, kuma ta mika goron gayyata ga Guterres don ya halarta. Da take yin la'akari da tashe-tashen hankula na baya-bayan nan, Emine Erdogan ta nuna alhininta game da barnar da yaƙe-yaƙe ke haifarwa, tana mai jaddada illar da ake yawan mantawa da ita ga yanayi da muhalli, wanda ke kara ta'azzara rikicin yanayi. Bayan taron, UWargidan Erdogan ta wallafa a X, inda ta kira tattaunawarta da Guterres da "mai amfani" tare da jaddada aniyarsu ta kokarin kawar da bola a duniya.